Bola Tinubu Ya Fada Mani Wanda Yake So Ya Zama Shugaban Majalisa In Ji Sanata Ndume

Bola Tinubu Ya Fada Mani Wanda Yake So Ya Zama Shugaban Majalisa In Ji Sanata Ndume

  • Muhammad Ali Ndume ya ce Bola Ahmed Tinubu yana goyon bayan takarar Sanata Godswill Akpabio
  • Sanata Ndume ya ce alamu na nuna tsohon Gwamnan Akwa Ibom zai doke Abdulaziz Yari a Majalisa
  • ‘Dan majalisar ya ce a halin yanzu Shugaban kasa, jam’iyyar APC da Sanatoci 75 su na goyon bayan Akpabio

Abuja - Muhammad Ali Ndume ya shaida cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya fada masa Godswill Akpabio ne ‘dan takaransa na shugaban majalisa.

Sanata Muhammad Ali Ndume ya fadawa tashar Channels cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna masa yana goyon bayan Godswill Akpabio.

Baya ga haka, Sanatan na Kudancin Borno ya ce shi aka bukaci ya jagoranci yakin zaben Akpabio.

Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a taro Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

‘Dan majalisar ya na mai sa ran cewa shugaban kasar ba zai canza ra’ayinsa ba, zai cigaba da goyon bayan Sanatan Arewa maso yammacin Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Umarci Shettima Ya Fito da Tsarin Taimakon Talaka Bayan Janye Tallafin Fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ndume wanda ya sha miya a majalisar tarayya ya kuma nuna cewa a cikin zababbun Sanatoci 109 da ake da su, mutane 75 duk su na bangarensu.

Takarar Abdulaziz Yari ta shugabancin majalisa

Amma duk da haka, ‘dan majalisar ya tabbatar da cewa su na fuskantar barazana daga tsaginsu domin tsohon Gwamna Abdulaziz Yari da ya fito takara.

Sai dai Sanatan na APC ya ce tsohon Gwamnan jihar Akwa Ibom ya sha gaban Yari a takarar.

"A yau dinnan, ina fada maka mu na da Sanatoci 75. Mu ne ke kan gaba. Mu na da goyon bayan jam’iyya, shugaban kasa yana mara mana baya.
Sannan mafi muhimmanci kuma, mu na da goyon bayan mafi yawan Sanatoci. Sanatocin nan sun sa hannu, duk su na goyon bayan tafiyarmu."

- Sanata Muhammad Ali Ndume

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Mambobi 67 Na Bayan Yari, Abdul Ningi Ya Ce Dole a Bar ’Yan Majalisa Su Zabi Son Ransu

Siyasa mugun wasa; batun takarar majalisa

An rahoto Ali Ndume ya na cewa Sanatan da yake goyon baya ya yi wa Yari zarra ta fuskar siyasa da kwakwalwa, ya na ganin zai yi wahala su rasa kujerar.

A siyasa komai yana iya canzawa a mintin karshe, Sanatan na Borno ya ce bai son ya cika-baki a kan zaben, amma yana sa ran su yi galaba a majalisar kasar.

Tinubu ya ba NEC aiki

An samu labari Gwamnatin Bola Tinubu za ta kara albashin ma’aikata, za a kawowa talaka sa’ida domin a samu saukin rayuwa bayan janye tallafin fetur.

A halin yanzu, Sanata Kashim Shettima ya ke rike da majalisar NEC mai kula da tattalin arzikin Najeriya, shi zai jagoranci yadda za a bullowa lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng