Matashi Mai Hannu Daya Ya Nuna Bajintarsa a Harkar Kwallon Kafa, Bidiyon Ya Yadu

Matashi Mai Hannu Daya Ya Nuna Bajintarsa a Harkar Kwallon Kafa, Bidiyon Ya Yadu

  • Bidiyo ya hasko wani matashi mai hannu daya yana sarrafa kwallon kafa cike da kwarewa
  • A cikin bidiyon, an gano matashin yana jefa kwallon daga bayan kafarsa sannan ya barta a iska
  • Ya kai kwallon har zuwa inda yake son ya kai kuma mutanen da ke kallo sun tafa tare da jinjina masa

Wani bidiyon TikTok da ya yadu ya nuno wani matashi mai hannu daya yana buga kwallon kafa cike da kwarewa.

Mutumin wanda ba a bayyana suna da shekarunsa ba ya nuna kwarewarsa a gaban dandazon jama'a da ke ta tafa masa tare da jinjina masa.

Matashi yana buga kwallon kafa
Matashi Mai Hannu Daya Ya Nuna Bajintarsa a Harkar Kwallon Kafa, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @love4ever
Asali: TikTok

Bidiyon, wanda ya samu fiye da 'likes' 300,000 da martanoni masu yawan gaske, ya fara da nuno matashin yana jefa kwallo daga kafarsa ta baya sannan ya ci gaba da barinsa a iska.

Kara karanta wannan

Daga Bata Kyautar Piya Wata 1, Matashiya Ta Yi Wa Wani Saurayi Kyautar Bazata a Bidiyo

Daga nan sai ya jujjuya kwallon da kafarsa, ya sa ya tafi inda yake so. Har ma ya kama kwallon da kansa ya sake jefa shi don ci gaba da wasan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bajintar da mutumin ya nuna ya burge masu kallo da yawa wadanda suka jinjinawa baiwar da Allah ya yi masa. Wasu sun yi martani cewa zai zama madubin duba ga mutanen da ke da nakasa.

Kwallon kafa na da farin jini sosai musamman a tsakanin matasa kuma yana nisadantar da kowa.

Mutumin TikTok din ya tabbatar da cewar babu abun da zai hana shi buga wasan da yake matukar so da nishadantuwa da shi.

Ya kuma nuna cewa kwallon kafa ba wai jefa kwallo a raga bane, illa nuna hikima da soyayyar abun.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Kara karanta wannan

An Samu Matsala: Dan Najeriya Ya Shiga Tashin Hankali Bayan Ya Gano Kullum Da Tsakar Dare Motarsa Tana Kunna Kanta

@ajudasvilanculos ya yi martani:

"Cr7, Neymar, Messi ku zo ka gani."

@abdulhakimissaka3 ya rubuta:

"Ya zama dole wannan ya shiga kundin tarihi na duniya."

@kudzawusaviour5 ya ce:

"Afrika ce ainahin gidan yan baiwa."

Matashi ya samu sha-tara ta arziki bayan ya yi wa wata matashiya kyautar piya wata daya

A wani labari na daban, wata matashiya ta gwangwaje wani matashi mai sana'ar piya wata da sha-tara ta arziki bayan ya yi mata kyautar ruwa leda daya.

Matashiyar ta roki matashin cewa ya bata ruwa tana jin kishirwa amma bata da kudi nan take ya mika mata, sai ta ba shi katan-katan na lemuka don ya kara jari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng