Majalisa Ta 10: Doguwa Ya Roƙi Yan Majalisu Dangane Da Zaben Da Ke Tafe
- Alhassan Ado Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta 9, ya roki ‘yan kungiyar G7 da su janye takararsu ga dan takarar jam’iyyar APC, Tajudeen Abass
- Doguwa ya bukaci ‘yan majalisar da su muhimmantar da sauyin shugabancin majalisar na yanzu da ake shirin yi zuwa na majalisa mai zuwa
- Mataimakin kakakin majalisar Idris Wase, ya ki amincewa da rokon na Doguwa, yana mai cewa, ubangidansa a siyasa, Solomon Lar, ya hango masa zama kakakin majalisa
Abuja - Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta 9, Alhassan Ado Doguwa ya roki mambobin G7 masu neman kujerar kakakin majalisar wakilai ta 10 mai zuwa da su janye wa dan takarar jam’iyyar APC, Hon Tajudeen Abass.
Doguwa ya yi wannan roƙon ne a yayin zama na bankwana da majalisar wakilan ta gudanar, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Ya ce ya kasance ɗaya daga cikin ’yan takarar da daga baya suka janyewa Abass domin ganin an yi komai lami lafiya.
Doguwa ya roƙi waɗanda ke takara su haƙura su janyewa Tajuddeen
Doguwa ya roƙi sauran 'yan majalisun da har yanzu suke takarar da su yi duba da idon basira, sun janye takarar tasu ga Tajuddeen Abass.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Doguwa ya bayyana cewa duk da dai ya so ya zama kakakin, kuma ya san ya cancanta, amma haka nan ya haƙura ya janye takarar ta sa domin a samu maslaha.
A kalamansa:
“Da haka ne nake kira ga ‘yan uwana mambobi, waɗanda har yanzu ke fafutukar neman kujerar, da su yi tunani, su ma su janye takarar da suke yi domin a samu sauyin shugabancin zuwa majalisa ta gaba cikin kwanciyar hankali.”
Majalisa Ta 10: Mambobi 67 Na Bayan Yari, Abdul Ningi Ya Ce Dole a Bar ’Yan Majalisa Su Zabi Son Ransu
“Ina yin hakan ne saboda ina cikin mambobin da a farko suka fara tsayawa takarar Shugaban majalisar. Mai girma shugaban majalisa, kuma ni na san cewa na cancanci zama kakakin majalisa.”
"Na yi imani da cewa, shugabancin majalisa abu ne daga Allah, da kuma amincewar ‘yan majalisar wakilai. Ba za a iya samun kakakin majalisa biyu ba a lokaci guda”.
Daily Trust a wani rahoto ta kawo cewa Doguwa tare da wasu 'yan majalisu 5 na APC ne suka janye takararsu ga Tajuddeen Abbas.
Idris Wase ya yi watsi da roƙon da Doguwa ya yi
Sai dai da yake jawabi nan take bayan Doguwa ya gama jawabi, mataimakin tsohon kakakin majalisar kuma mamba a ƙungiyar G7, Hon. Idris Wase ya ki amincewa da roƙon, yana mai cewa zai ci gaba da takarar har zuwa ƙarshe.
A cewarsa, burinsa na zama kakaki, wani hangen nesa ne da wani tsohon gwamnan jihar Filato, Solomon Lar, wanda ya kira da ubangidansa ya yi.
Yari ya kai wa Buhari ziyara a Daura
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa muku, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar ya kai wa Buhari ziyara a gidansa da ke Daura.
An ce ziyarar ta Yari na da alaƙa da takarar shugabancin majalisar dattawa da yake yi a yanzu.
Asali: Legit.ng