Femi Gbajabiamila Ya Rusa Majalisa Ta 9, Zai Kama Aiki A Fadar Shugaban Kasa
- Majalisar wakilai ta Tarayya ta gabatar da zamanta na karshe a yau Laraba 7 ga watan Yuni don ba da dama ga sabuwar majalisar ta 10
- Kakakin majalisar ya yi bankwana da kuma jawabinsa na karshe yayin da ya rusa majalisar ta 9 don ba wa sabuwar majalisar dama
- Shugaba Bola Tinubu a ranar Juma’a 2 ga watan Yuni ya nada Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan Gwamnatin Tarayya
FCT, Abuja – A wani yanayi da ba a saba gani ba, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya ce mambobin majalisar sun yi iya kokarinsu don gina kasa da kawo ci gaba.
Femi ya jagoranci ganawarshi ta karshe da majalisar a ranar Laraba 7 ga watan Yuni cikin jimami.
Wannan na zuwa ne bayan tsohon kakakin ya rusa gudanarwar majalisa ta 9, bayan da Shugaba Tinubu ya nada shi a matsayin shugaban ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.
Majalisa Ta 10: Mambobi 67 Na Bayan Yari, Abdul Ningi Ya Ce Dole a Bar ’Yan Majalisa Su Zabi Son Ransu
Femi ya jagoranci majalisar na tsawon shekaru hudu daga 2019 zuwa 2023
Gbajabiamila wanda shi ne kakakin majalisar tun shekarar 2019 zuwa 2023 ya rusa majalisar ta 9 a yau, cewar Legit.ng.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Honarabul Ado Doguwa ya ba da damar fara zaman majalisar na karshe, yayin da Honarabul Ndudi Elumelu wanda shi ne shugaban marasa rinjaye ya goyi baya.
Gbaja ya yi bankwana cikin yanayi mai ratsa zuciya a zamansa na karshe
A cikin wani yanayi mai sosa zuciya, Femi ya ce:
“Zan yi kewar wannan majalisar da ku baki daya, ba zan iya kwatanta godiyar da zan muku ba yadda kuka ba da gudumawa a wannan majalisa, mun zo, mun kuma gani amma har yanzu ba mu yi nasara ba, yadda nake son aiki anan bai sauya ba.”
Har ila yau, Shugaba Tinubu ya rantsar da George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), bayan nada shi a ranar Juma’a 2 ga watan Yuni, Akume ya yi alkawarin ba zai bai wa ‘yan Najeriya kunya ba.
Tsohon gwamnan jihar Benue ya bayyana haka ne yayin ganawa da ‘yan jaridu bayan an rantsar da shi a yau Laraba 7 ga watan Yuni, cewar Vanguard.
Tinubu Ya Ba Wa Lawan Da Gbajabiamila Sabon 'Aiki' Mai Muhimmanci
A wani labarin, Shugaba Tinubu ya bukaci shugabannin majalisun Tarayya su nemo mafita akan rikicin shugabanci.
Tinubu ya bukaci hakan ne bayan rikicin shugabanci ya mamaye dukkan majalisun guda biyu.
Asali: Legit.ng