Gwamnan Jihar Niger Ya Rantsar Da Sakataren Gwamnatin Jihar Da Wasu Muhimman Mukamai Da Ya Nada

Gwamnan Jihar Niger Ya Rantsar Da Sakataren Gwamnatin Jihar Da Wasu Muhimman Mukamai Da Ya Nada

  • Jihar Niger ta yi sabon sakataren gwamnatin jihar da shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar da wasu muhimman muƙamai
  • Gwamnan jihar Mohammed Umaru Bago bayan ya rantsar da su ya buƙace su da su jajirce wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu
  • Gwamna Bago ya kuma bayar da tabbacin cewa naɗe-naɗen da zai yi na gaba mata zai ba domin cika alƙawarin da ya ɗauka lokacin kamfe

Jihar Niger - Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umaru Bago ya rantsar sakataren gwamnatin jihar (SSG), shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar da shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa ya rantsar da su ne bayan ya gama nazari kan cancantarsu, ƙwarewarsu da gaskiyarsu domin yi wa jihar aiki, rahoton Tribune ya tabbatar.

Gwamna Bago ya rantsar da sabon sakataren gwamnatin jihar
Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umaru Bago Hoto: Mohammed Umaru Bago
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan mai shari'a Hassana Bawa Wuse ta rantsar da su a madadin alƙalin alƙalan jihar, mai shari'a Halima Ibrahim Abdulmalik, a ɗakin taro na fadar gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Rigima Sabuwa: Gwamnan PDP Zai Yi Binciken Kwakwaf Kan Gwamnatin Da Ya Gada, Ya Bayyana Dalilansa

Gwamnan ya kuma ƙara da cewa gwamnatinsa za ta dama sosai da matasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bago ya ƙara da cewa waɗanda ya ba muƙaman zaɓinsa ne kuma suna da ƙwarewa da cancantar gudanar da ayyukansu inda ya buƙace su da su ba mara ɗa kunya wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyan su, cewar rahoton Daily Post.

Zai naɗa mata muƙamai a gwamnatinsa

Ya kuma ƙara da cewa naɗe-naɗen da zai yi guda biyar na gaba, mata zai ba domin cika alƙawarin da ya ɗauka a wajen yaƙin neman zaɓe na kawo daidaito da tafiya da kowa a gwamnatinsa.

Waɗanda suka yi rantsuwar kama aikin sun haɗa da Engr. Abubakar Salisu a matsayin shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, Hon. Usman Abdullahi Batamangi a matsayin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar (CoS).

Sauran sun haɗa da Sadiq Yusuf a matsayin mataimakin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar, da Bello Ibrahim a matsayin mataimakin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar na mataimakin gwamna.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Muhimman Abubuwan da Su Wike Suka Tattauna da Shugaba Tinubu a Aso Rock Sun Bayyana

Tinubu Ya Rantsar Da Sabon SGF

Rahotanni sun zo cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabon sakataren gwamnatin tarayya (SGF).

Sanata George Akume ya yi rantsuwar kama aiki a fadar shugaban ƙasa da ke a birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel