A Karon Farko, Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa Da Gwamnonin Jihohi a Abuja
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga taro da kafatanin gwamnonin jihohi 36 na ƙasar nan a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja
- Wannan ne karo na farko da sabon shugaban kasa ya gana da gwamnonin tun bayan kama aiki a ranar Litinin, 29 ga watan Yuni, 2023
- Rahoto ya nuna cewa baki ɗaya gwamnoni a karkaashin ƙungiyarsu sun halarci taron amma guda biyu sun turo mataimakansu su wakilce su
FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yanzu haka ya shiga gana wa da gwamnonin jihohi a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.
Jaridar The Cable ta ce wannan zama shi ne karo na farko da shugaba Tinubu ya yi da kafatanin gwamnonin jihohin ƙasar nan 36 tun bayan da ya karɓi rantsuwar kama aiki.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa taron ya fara ne da misalin ƙarfe 12:36 na tsakar rana yau Laraba, 7 ga watan Yuni, 2023.
Gwamnonin jihohin Zamfara, Kano, Taraba, Kogi, Ogun, Nasarawa, Bayelsa, Adamawa, Ebonyi, Legas, Ribas, Osun, Jigawa, Benuwai, Taraba, Delta, da jihar Enugu duk sun halarci taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran jihohin da gwamnoninsu suka shiga ganawa da shugaban kasan su ne, Kuros Riba, Oyo, Filato, Kebbi, Abiya, Imo, da kuma jihar Bauchi.
Sai dai mataimakan gwamna a jihohin Edo da kuma Neja ne suka wakilci shugabannin su a wurin taron.
Haka nan kuma mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima da kuma Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), George Akume, sun halarci ganawar yau Laraba.
Taron ya fara ne jim kaɗan bayan sabon sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya karɓi rantsuwar kama aiki.
Gwamnonin sun shiga wannam ganawa ne karƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa (NGF) wacce gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak ke shugabanta.
Idan baku manta ba a ranar Jumu'a da ta gabata, shugaba Tinubu ya gana da gwamnonin jam'iyyar APC karƙashin ƙungiyar gwamnonin ci gaba (PGF), kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnan Benue Ya Kori Ma'aikata daga Aiki
A wani rahoton na daban kuma Gwamnan Benue ya kori ma'aikatan Ortom ya ɗauka gab da zai sauka mulki.
Gwamna Alia na jihar Benuwai ya sallami ma'aikatan da Ortom ya dauka gab da sauka mulki, ya kuma rushe kara matsayi, da ƙara wa wasu manyan ma'aikata wa'adin ritaya.
Asali: Legit.ng