Gwamnan Benue Ya Kori Ma'aikatan Ortom Ya Dauka Dab da Zai Sauka Mulki
- Sabon gwamnan jihar Benuwai na jam'iyyar APC ya soke duk wasu matakai da tsohon gwamnan da ya gaba, Samuel Ortom, ya ɗauka dab da zai sauka
- Rabaran Hyacinth Alia, a wata sanarwa ranar Laraba, ya sallami dukkan ma'aikatan da Ortom ya ɗauka dab da zai bar mulki
- Haka nan ya soke canjin wurin aikin da tsohon gwamnan ya yi wa ma'aikata tun daga watan Octoba, 2022 zuwa yau
Benue - Gwamnan jihar Benuwai, Rabaran Hyacinth Alia, ya kori ma'aikatan da tsohon gwamnan da ya sauka kwanan nan, Samuel Ortom, ya ɗauka yana dab da sauka daga mulki.
Gwamna Alia ya ce, "Duk ma'aikatan da gwamnatin da ta gabata ta ɗauka daga watan Mayu, 2023 zuwa yau mun kore su daga aiki kuma matakin zai fara aiki nan take."
Yadda aka samu saɓani tun farko
Punch ta ce idan baku manta ba, gabannin rantsar da sabon gwamna, jam'iyyar PDP mai mulki aa wancan lokacin da APC sun riƙa musayar kalamai masu zafi kan sabbin tsare-tsaren da gwamnatin Ortom ta ɓullo da su.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Manyan jam'iyyun sun rika jifar juna da kalamai masu ɗumi bisa matakin da Ortom ya riƙa dauka gab da karewar wa'adinsa, kama daga ɗaukar sabbin ma'aikata, kara wa ma'aikata matsayi da ba da kwangiloli.
Jam'iyyar APC ta bakin mai magana da yawunta, Daniel Ihomun, ta zargi gwamnatin Ortom a wancan lokaci da yunkurin kulla gadar zare ga sabuwar gwamnati mai zuwa.
Sai dai a bangarenta, PDP ta bakin kakakinta, Bemgba Iortyom, ta maida martani da cewa Ortom ne gwamna mai cikakken iko a jihar Benuwai har zuwa ranar miƙa mulki, 29 ga watan Mayu, 2023.
Sabon gwamna ya soke naɗe-naɗe da ɗaukar aikin da Ortom ya yi
Amma a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamna, Kula Tersoo, ya fitar ranar Laraba, 7 ga watan Yuni, Gwamna Alia ya soke dukkan ma'aikatan da Ortom ya ɗauka aiki.
Ya kuma umarci dukkan waɗanda suka kai lokacin ritaya daga aiki kuma basu bar Ofis ba saboda an ƙara musu wa'adi ko an ɗauke su aikin kwantiragi da su gaggauta miƙa takardar aje aiki.
Wani sashin sanarwan ya ce:
"Duk wasu ma'aikata da lokacin ritayarsu ya yi amma har yanzun ba su miƙa takardar aje aiki ba su gaggauta yin hakan nan take."
"Haka nan duk ma'aikata ko mutanen da aka naɗa manyan Sakatarori daga watan Janairu, 2023 zuwa yau su koma asalin matsayin da su ke."
"Sannan duk ma'aikatan da aka sauya wa wurin aiki daga watan Oktoba, 2022 zuwa yau mun soke matakin, duk wanda hakan ta faru a kansa ya koma wurin aikinsa na baya daga yanzu."
Gwamnan Arewa Ya Gana da Shugabannin Tsaro Bayan Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka 37, Ya Ɗauki Matakai Masu Kyau
Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Gwamnonun Jihohi a Abuja
A wani labarin kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawa yan,u haka da baki ɗaya gwamnonin jihohin Najeriya.
Wannan zama shi ne karo na farko da shugaba Tinubu ya yi da kafatanin gwamnonin jihohin ƙasar nan 36 tun bayan da ya karɓi rantsuwar kama aiki.
Asali: Legit.ng