Obasa Ya Sake Samun Nasarar Zama Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Legas

Obasa Ya Sake Samun Nasarar Zama Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Legas

  • Dakta Mudashiru Ajayi Obasa, ya sake samun nasarar zama kakakin majalisar dokokin jihar Legas karo na uku a jere
  • Bayanai sun nuna tun a shekarar 2015, Obasa ya hau karagar shugabancin majalisar dokokin, ya sake komawa karo na biyu a 2019
  • Majalisar dokokin Legas ta ƙunshi mambobi 40, amma a wannan karon 20 ne suka samu nasarar dawowa yayin da 20 kuma sabbin zuwa ne

Lagos - Ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Agege 01, Dakta Mudashiru Ajayi Obasa, ya sake lashe zaɓen kakakin majalisar dokokin jihar Legas ta 10, kamar yadda Punch ta tattaro.

Mamban majalisar na tsawon zango shida zai sake shugabantar majalisar dokokin Legas karo na uku kenan a jere tun bayan lokacin da aka fara zabensa a matsayin kakaki a 2015.

Obasa.
Obasa Ya Sake Samun Nasarar Zama Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Legas Hoto: Punchng
Asali: UGC

Mamba mai wakiltar mazaɓar Ifako Ijaiye 01, Honorabul Adewale Temitope Adedeji, ne ya fara gabatar da Obasa a matsayin wanda ya cancanta ya ci gaba da shugabanci.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa: Cikakkun Bayanai Kan Ziyarar Yari Wajen Buhari a Daura Sun Bayyana

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hakan ta faru ne bayan gwamna Babajide Sanwo-Olu, ya rantsar da sabuwar majalisar ta 10.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga nan ne sai ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Epe II, Ogunkelu Sylvester Oluwadahunsi, ya goyi bayan sake naɗa Obasa a matsayin kakaki. Babu wanda ya yi jayayya.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa majalisar dokokin jihar Legas ta 10 da ta fara aiki ta ƙunshi yan majalisun jiha daga mazaɓu daban-daban guda 40.

Haka nan kuma jam'iyyar All Progressives Congress, (APC) mai mulki ce ta mamaye majalisar, tana da mambobi 38 yayin da jam'iyyar Labour Party ke da guda biyu.

Daga cikin waɗan nan yan majalisa 40, 20 daga cikinsu sun samu nasarar ta zarce yayin da 20 kuma wannan ne karo na farƙo da zasu shiga majalisar bayan lashe zaɓe a 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC Sun Fadi Waɗanda Suka Fi Cancanta da Shugabancin Majalisar Tarayya

Gwamnan Sakkwato Ya Gana da Shugabannin Tsaro

A wani labarin kuma Gwamnan Sakkwato ya gana da shugabannin tsaro kan harin da yan bindiga suka kai, inda suka kashe mutane 37.

Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya katse tafiyar da ya yi saboda harin da yan bindiga suka kai jiharsa ranar Asabar da ta gabata.

Gwamnan ya gana da shugabannin hukumomin tsaro na jiha, ya ɗauki matakai masu kyau domin kawo karshen ayyuna 'yan bindiga a faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262