Shugaba Tinubu Ya Ba Wa Lawan Da Gbajabiamila Sabon 'Aiki' Mai Muhimmanci

Shugaba Tinubu Ya Ba Wa Lawan Da Gbajabiamila Sabon 'Aiki' Mai Muhimmanci

  • Shugaba Bola Tinubu ya nemi Femi Gbajabiamila da Ahmed Lawan da su tabbatar an samu maslaha wajen rabon mukamai a majalisa ta 10
  • An ruwaito cewa Tinubu ya bukaci Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai da su tabbatar ba a samu yan takara biyu a neman shugabancin majalisun ba
  • Tinubu ya bukaci haka a wata ganawar sirri da ya yi da shugabannin majalisun biyu

Aso Villa, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya sake yin wani sabon yunkuri game da rikicin rabon mukamai a majalisa da ya mamaye APC a neman shugabancin majalisar ta 10.

An ruwaito shugaban ya bukaci Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa; da Femi Gbajabiamila, Kakakin Majalisar Wakilai, da su kawo mafita kan rikicin, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hotuna Sun Bayyana Yayin da Shugaban Ma’aikatan Buhari Ya Mika Mulki Ga Femi Gabjabiamila

Shugaba Tinubu ya ba Lawan da Gbaja sabon aiki
Tinubu ya ce Lawan da Gbaja su warware matsalar shugabancin majalisa. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Tinubu ya fadawa Lawan, Gbajabiamila a tattaunawa ta musamman

An ruwaito cewa shugaban ya bada umarni ga Lawan da Gbajabiamila a tattaunawar da suka yi a fadar shugaban kasa ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni.

Rahoton ya ce Tinubu ya shiga maganar biyo bayan korafi kan batun rabon mukaman zuwa shiyya-shiyya ga jam'iyya mai mulki a majalisun kasar nan.

An ce Tinubu ya umarci shugabannin majalisun su samar da mafita don gudun rikici tsakanin zababbun sanataoci.

Tinubu ya bukaci Lawan, Gbajabiamila da kada su bari APC ta gabatar da yan takara biyu a neman shugabancin majalisar

A cewar majiyar da ke da kusanci da fadar shugaban kasa, Tinubu ya bukaci Lawan da Gbajabiamila su tabbatar jam'iyyar APC bata gabatar da yan takara biyu ba a zaben shugabancin majalisun ranar 13 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Labari Da Duminsa: Tinubu Ya Sanar Da Nadin Gbajabiamila A Hukumance, Tsohon Mataimakin Gwamnan Jigawa Ya Samu Mukami Shima

An kuma bayyana cewa an shaidawa shugaban kasar cewa ba yadda za a yi a raba kujerun biyu zuwa zuwa shiyyar Arewa maso yamma a kuma hana Arewa ta tsakiya sannan kuma a samu nasara.

Majiyar ta ce:

"Shugaban ya ba wa shugabannin majalisun, aikin daidaita rikicin karba-karba na shiyya a shugabancin majalisar da jam'iyyar APC ta fitar a watan da ya gabata."

Shugaban ma'aikatan Tinubu: Gbajabiamila ya bayyana abu na gaba bayan lashe zabe karo na 6

Legit.ng ta ruwaito cewa Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya magantu kan sabon nadin Shugaban Ma'aikatar Fadar Shugaban Kasa da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya masa.

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana Gbajabiamila a matsayin shugaban ma'aikata a lokacin da yake tattauna da gwamnonin APC a fadar shugaban kasa ranar Juma'a.

Shugaban majalisar ya gode wa shugaban kasa bisa sabon mukamin tare da yin alkawarin aiki da shugaban kasar daga 14 ga watan Yuni kamar yadda aka bukata a takardar da aka aika masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164