Hotuna Sun Bayyana Yayin da Gambari Ya Mika Mulki Ga Gabjabiamila a Matsayin Sabon Shugaban Ma’aikata

Hotuna Sun Bayyana Yayin da Gambari Ya Mika Mulki Ga Gabjabiamila a Matsayin Sabon Shugaban Ma’aikata

  • Shugaban ma'aikatan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari, ya mika mulki ga magajinsa, Femi Gbajabiamila
  • An yi bikin mika mulkin ne a fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 5 ga watan Yuni, a gaban shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Hakan na zuwa ne yan makonni gabannin 14 ga watan Yuni, lokacin da zai fara aiki a sabon matsayinsa na shugaban ma'aikatan shugaban kasa

Ibrahim Gambari, shugaban ma'aikatan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya mika mulki ga magajinsa, Femi Gbajabiamila.

Bikin mika mulkin wanda ya samu halartan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya gudana ne a ranar Litinin, 5 ga watan Yuni a fadar shugaban kasa da ke Abuja, jaridar The Cable ta rahoto.

Farfesa Ibrahim Gambari, Shugaban kasa Bola Tinubu da Femi Gbajabiamila
Hotuna Sun Bayyana Yayin da Gambari Ya Mika Mulki Ga Gabjabiamila a Matsayin Sabon Shugaban Ma’aikata Hoto: Speaker Femi Gbajabiamila
Asali: Facebook

Ibrahim Gambari ya mika mulki ga Femi Gbajabiamila a matsayin sabon shugaban ma'akatan shugaban kasa

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku Ya Lissafa Jerin Mukamai 5 Da Bai Kamata Shugaban Kasa Tinubu Ya Ba Yan Siyasa Ba

An sanar da Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai mai barin gado a matsayin sabon shugaban ma'aikatan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Juma'a, 2 ga watan Yuni.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A bikin mika mulki, wanda aka nada a wani bidiyo, ya nuno shugaban kasar a wajen daukar hotuna tare da tsoho da sabon shugaban ma'aikata, jaridar Daily Trust ta rahoto.

A halin da ake ciki, Gbajabiamila zai kama aiki a matsayin sabon shugaban ma'aikatan shugaban kasa a ranar 14 ga watan Yuni.

Dino Melaye ya kalubalanci Gwamna Makinde da ya halarci zaman kotun zaben shugaban kasa don marawa Atiku baya

A wani labari na daban, Dino Melaye, dan takarar gwamna na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben jihar Kogi, ya fada ma Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da ya tabbatar da kalamansa na cewa jam'iyyar ta fara farfado da kanta.

Kara karanta wannan

Sabuwar Gwamnati: Jerin Sunayen Wadanda Tinubu Ya Ba Wa Mukami a Makonsa Na Farko

Melaye ya kalubalanci Makinde da ya halarci zaman kotun zaben shugaban kasa na 2023 a Abuja, don nuna goyon baya ga Atiku Abubakar, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023.

Dan takarar gwamnan na PDP ya bukaci hakan ne da yake martani ga jawabin Makinde na cewar jam'iyyar ta fara warkewa da kanta gabannin tattaunawar gaba yayin wani taro da babbar jam'iyyar adawar ta gudanar a jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng