Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Wike, Umahi da Akpabio a Villa

Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Wike, Umahi da Akpabio a Villa

  • Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga taro yanzu haka tare da tsoffin gwamnoni uku a fadarsa ta Abuja
  • Rahoto ya nuna tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike, tsohon gwamnan Ebonyi, Dave Umahi da Godswill Akpabio sun isa Villa da karfe 2:33 na rana
  • Ana tsammanin ganawar ba zata rasa alaka da batun naɗa ministoci da kuma shugabannin majalisa ta 10 ba

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawa da tsoffin gwamnoni uku yanzu haka a fadarsa Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja.

Tsoffin gwamnonin da suka haɗa da Nyesom Wike na jihar Ribas, Dave Umahi na jihar Ebonyi da Godswill Akpabio na Akwa Ibom sun isa fadar da misalin karfe 2:33 na rana.

Shugaba Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Wike, Umahi da Akpabio a Villa Hoto: @ABAT
Asali: Twitter

Vanguard ta rahoto cewa da farko jami'an tsaro sun dakatar da su domin tabbatar da batun zuwansu daga sama kafin daga bisani jiga-jigan uku suka wuce zuwa ofishin shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wasu 'Yan Daba Sun Farmaki Ayarin Gwamnan Arewa a Hanyar Dawowa Daga Abuja

Wike da Umahi (zababben sanata a inuwar APC) sun kai ziyara fadar shugaban ƙasa makon da ya gabata amma a lokuta daban-daban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane muhimmin batu zasu tattauna a taron?

Rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa har kawo yanzu ba'a bayyana muhimman batutuwan da Tinubu zai tattauna da jiga-jigan siyasan ba a hukumance.

Sai dai ana ganin wannan gana wa ba zata rasa alaƙa da kokarin zakulo ministoci da kuma zaɓen shugabannin majalisar tarayya ta 10 da ke ƙara matsowa ba.

Sanata Akpabio, wanda ya samu goyon bayan jam'iyar APC mai mulki, ana hasashen ya shiga tawagar ne domin kara jaddada burinsa na zama shugaban majalisar dattawa ta 10.

Haka nan wani rahoto ya yi ikirarin cewa da yuwuwar gwamnatin Tinubu ta duba bai wa Wike muƙamin Minista bisa gudummuwar da ya bayar a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Shugaba Tinubu, Wike Ya Fayyace Gaskiya Kan Yuwuwar Ya Koma Jam'iyyar APC

Idan baku mata ba, duk da Wike mamban jam'iyyar PDP ne amma ya goyi bayan takarar Bola Ahmed Tinubu, wanda ya samu nasara da ƙuri'u masu rinjaye a jihar Ribas.

Gwamnan APC Ya Sa Labule da Shugabannin Kwadugo Kan Cire Tallafin Mai

A wani rahoton na daban kuma Gwamnan Kaduna ya gana da wakilan ƙungiyoyin ƙwadugo kan cire tallafin man fetur a Najeriya.

Ana tsammanin a wurin ganawar Malam Sani da jagororin NLC, za su kafa kwamitoci biyu da zasu zauna su yi nazarin hanyoyin magance wahalhalun da jama'a zasu shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262