PDP, Labour Party Sun Taso Shugaba Tinubu a Gaba Kan Jan Kafa Wajen Bayyana Kadarorinsa

PDP, Labour Party Sun Taso Shugaba Tinubu a Gaba Kan Jan Kafa Wajen Bayyana Kadarorinsa

  • An caccaki shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima bisa jan ƙafar da suke yi wajen bayyana kadarorinsu
  • Jam'iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da Labour Party sun buƙaci shugaban ƙasar da ya bayyana kadarorinsa a idon duniya
  • An buƙaci Tinubu da ya yi koyi da tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar'adua wanda ya bayyana kadarorinsa a idon duniya

FCT, Abuja - An buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya yi koyi da marigayi Umaru Musa Yar'adua wajen bayyana kadarorinsa a idon duniya.

Kakakin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Debo Ologunagba, shi ne ya yi wannan kiran a ranar Lahadi, 4 ga watan Yunin 2023.

PDP da LP sun bukaci shugaba Tinubu ya bayyana kadarorinsa
Shugaban kasa, Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cewar jaridar Punch, Ologunagba ya bayyana cewa yakamata shugaban ƙasar da mataimakinsa su cika fom ɗin da hukumar ɗa'ar ma'aikata ta basu domin bayyana kadaorinsu, saboda doka ta buƙaci hakan.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Buhari Ya Yi Watsi Da Kudirin Yari Da Kalu Na Shugabancin Majalisa, Ya Bayyana Kwararan Dalilansa

A kalamansa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Yakamata su yi koyi da tsohon shugaban ƙasa, marigayi Umaru Musa Yar'adua wajen nunawa ƴan Najeriya cewa a shirye suke su gudanar da mulki na gaskiya."
"Akwai tanadin doka kan bayyana kadarori na masu riƙe da muƙamai, haƙƙi ne wanda ya zama tilas."

Ologunagba ya ƙara da cewa duk da sun mayar da fom ɗin kadarorin na su, yakamata a nuna shi a idon duniya kowa ya gani.

Labour Party ta yi martani kan jan ƙafar Tinubu wajen bayyana kadarori

Jam'iyyar Labour Party yayin da ta ke martani kan jan ƙafar da shugaba Tinubu ya ke yi wajen bayyana kadaorinsa, tace yakamata a ba shi isashshen lokaci.

Shugaban jam'iyyar, Julius Abure, ya yi nuni da cewa Tinubu hamshaƙin attajiri ne, domin haka yana buƙatar lokaci mai yawa kafin ya kammala haɗa kadarorinsa.

Kara karanta wannan

Kalubale 10 Masu Hadari Da Tinubu Ya Tsallake Kafin Shiga Fadar Shugaban Kasa

"Mu ba shi lokaci domin ya bayyana kadarorinsa. Wannan shi ne ra'ayi na. Amma doka tace ya bayyana kadarorinsa. A ganina yakamata ya yi hakan a idon duniya." A cewarsa.
"Hamshaƙin attajiri ne saboda abubuwan da ya tara bayan ya yi sanata sannan ya yi gwamna har sau biyu. An ya kuwa zai iya tuna dukkanin kadarorinsa."

Kalubalen Da Tinubu Ya Tsallake Kafin Zama Shugaban Kasa

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya fuskanci ƙalubale da dama kafin ya samu nasarar ɗarewa kan shugabacin ƙasar nan.

Shugaban ƙasar ya tsallake ƙalubale aƙalla guda 10 da suka nemi su kawo masa cikas a burinsa na zama shugaban ƙasa bayan mulkin Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng