Gwamnonin APC Sun Gana da Tinubu, Sun Amince da Cire Tallafin Man Fetur

Gwamnonin APC Sun Gana da Tinubu, Sun Amince da Cire Tallafin Man Fetur

  • Kungiyar gwamnonin ci gaba ta tabbatar da goyon bayanta ga matakin shugaban kasa, Bola Tinubu, kan tallafin man fetur
  • Shugaban gwamnonin APC kuma gwamnan Imo, Hope Uzodinma, ne ya bayyana haka bayan ganawa da shugaba Tinubu a Aso Rock
  • Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda farashi ya yi tashin gwauron zabo lokaci guda daga jin kalaman Tinubu a wurin rantsuwa

Abuja - Gwamnonin ci gaba (PGF) sun nuna cikakken goyon bayansu ga matakin gwamnatin tarayya na cire tallafin Man Fetur a Najeriya.

The Nation tace gwamnonin, waɗanda suka ci zaɓe karkashin inuwar APC sun goyi bayan matakin ne yayin da suka ziyarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock.

Gwamnonin PGF.
Gwamnonin APC Sun Gana da Tinubu, Sun Amince da Cire Tallafin Man Fetur Hoto: @ABAT
Asali: Twitter

Sai dai gwamnonin sun bayyana takaicinsu bisa tashin farashin litar mai farat ɗaya biyo bayan kalaman shugaban kasa a wurin bikin rantsuwar kama aiki.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Kara Mafi Karancin Albashi? Shugaban Kasa Ya Yi Sabuwar Sanarwa

Da yake hira da 'yan jarida jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa, shugaban ƙungiyar gwamnonin ci gaba kuma gwamnan Imo, Hope Uzodinma, ya yi Alla-wadai da ƙara farashin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Uzodinma ya nuna damuwarsa bisa ƙara farashin mai kan abinda ya kira, "Tsohon kaya," da 'yan kasuwar Fetur suka yi awanni bayan kalaman Tinubu.

Haka nan ya yi kira ga ɗaukacin yan Najeriya su hakura su koma bayan matakin gwamnati na tsame hannu daga biyan maƙudan kuɗin tallafin man Fetur.

Asalin lokacin da FG ta cire tallafin mai

Uzodinma ya bayyana cewa kasafin kuɗin shekarar 2023 bai ware kuɗin biyan tallafin man Fetur har bayan watan Yuni ba, don haka ya kamata mutane su gane cewa Tinubu ya gaji cire tallafin ne.

A cewarsa, wannan tsadar farashin zata yo ƙasa da zaran 'yan kasuwa sun fara gasa a tsakaninsu da kuma fara aikin matatar man Ɗangote a watan Yuni, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Bayyana Wadanda Za Su Taimakawa Gwamnatinsa Samun Nasara

Shugaba Tinubu Ya Aike da Saƙo Mai Muhimmanci da Gwamnonin APC 3 da Wani Gwamnan PDP

A wani rahoton na daban Shugaba Tinubu ya aike da sakon taƴa murna ga gwamnoni 4 a Najeriya.

Tinubu ya aika sakon taya murnan ne kwanaki kalilan bayan an zaɓi sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya da shugaban gwamnonin jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262