Tinubu Ya Bayyana Wadanda Za Su Taimakawa Gwamnatinsa Samun Nasara

Tinubu Ya Bayyana Wadanda Za Su Taimakawa Gwamnatinsa Samun Nasara

  • Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana abin da gwamnonin Najeriya za su yi domin ganin ya gudanar da mulkinsa cikin nasara da kwanciyar hankali
  • Tinubu ya bayyana cewa duk wani hukunci ko mataki da gwamnonin za su ɗauka, zai iya taimakawa ko kawo cikas ga ci gaban ƙasar nan
  • Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da shugabannin kungiyar gwamnonin Najeriya da kuma gwamnonin APC

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana irin muhimmancin da gwamnonin Najeriya ke da shi wajen samun nasarar gwamnatin sa.

A cewar Tinubu, gwamnonin na da matukar muhimmanci ga nasarar da gwamnatinsa za ta samu a ƙasa baki ɗaya.

Tinubu ya fadi irin muhimmancin gwamnoni a gwamnatinsa
Tinubu ya ce gwamnoni na da matukar muhimmanci a gwamnatinsa. Hoto: Seyi Makinde, Abdulrahman Abdulrazaq, Hope Uzodimma, Buhari Sallau
Asali: Facebook

Tinubu ya taya sababbin shugabannin gwamnoni murna

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake taya sabbin shugabannin kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), Abdulrahman Abdulrazaq, gwamnan jihar Kwara, da Seyi Makinde, gwamnan Oyo murna, a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni, in ji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PGF Sun Ɗauki Matsaya Kan Batun Cire Tallafin Man Fetur a Najeriya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, shugaban ya kuma taya gwamnan Imo Hope Uzodinma da Uba Sani gwamnan Kaduna murnar zaɓarsu da aka yi a matsayin shugaba da mataimakin shugaban ƙungiyar gwamnonin APC.

A kalaman Tinubu:

"A matsayin shuwagabannin jihohi, gwamnoni na da matuƙar muhimmanci ga nasarar da gwamnatinmu za ta samu gaba ɗaya, da kuma muradinmu na samar da Najeriya da za ta yi wa kowa daɗi."
"A matsayin ginshiƙan ci gaba a cikin tafiyarmu zuwa samar da ƙasa mai wadata da aminci, abin da jihohi suka yi ko suka ƙi yi na da matuƙar tasiri."

Shugaba Tinubu ya nada tsohon ministan Buhari a matsayin SGF

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a ranar Juma’a, 2 ga watan Yuni, ya sanar da naɗin tsohon ministan ayyuka na musamman, George Akume, a matsayin sakataren gwamnatin tarayya (SGF).

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Aike da Saƙo Mai Muhimmanci da Gwamnonin APC 3 da Wani Gwamnan PDP

Tsohon gwamnan jihar Binuwai, wanda kuma ya yi aiki a ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin tsohon ministan ayyuka na musamman.

Wani mai taimakawa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Tolu Ogunlesi ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Tinubu ya naɗa Gbajabiamila shugaban ma'aikatan fadar gwamnati

A labarinmu na baya, kun ji cewa Tinubu ya sanar da naɗin tsohon kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, a matsayin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin ƙasar.

Haka nan Tinubun ya sanar da naɗin mataimakin tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia a matsayin mataimakin shugaban ma'aikatan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng