Majalisa Ta 10: ‘Ba Na Sha’awar Neman Kujerar Majalisa’, Ahmad Lawan Ya Fadi Dalilansa Na Kin Tsayawa Takara

Majalisa Ta 10: ‘Ba Na Sha’awar Neman Kujerar Majalisa’, Ahmad Lawan Ya Fadi Dalilansa Na Kin Tsayawa Takara

  • Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya bayyana cewa bai sha’awan neman kujerar majalisar dattawa a yanzu
  • Lawan ya fadi haka ne a ranar Alhamis 1 ga watan Yuni bayan ganawarsu da Shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima
  • Ya ce ba ya bukatar zama shugaban majalisar saboda ya bayar da gudumawar da ya kamata a majalisar ta dattawa

FCT, Abuja – Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya karyata jita-jitan da ake yadawa cewa yana son tsayawa takarar shugabancin majalisar.

Lawan ya fadi haka ne ga ‘yan jaridu bayan kammala ganawarsu da Shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis 1 ga watan Mayu.

Ahmad Lawan
Majalisa Ta 10: Ba Na Sha’awar Neman Kujerar Majalisa, Cewar Ahmad Lawan. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Ganawar ta samu halartar maitaimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Za Ta Sallami Wasu Sanatoci da ‘Yan Majalisa da Naira Biliyan 30

Ba na bukatar kujerar majalisa

Ya bayyana cewa bai taba nuna sha’awar neman takarar ba saboda ba ya bukata, ya ce bayan shafe shekaru 24 a majalisar, lokaci ya yi da ya kamata ya taimaka wa sabbin ‘yan majalisu da aka zaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Ba na bukatar zama shugaban majalisar, na ba da gudumawar da zan bayar, kuma ina murnar irin gudumawar da muka bayar, ban taba nuna sha’awan neman takarar ba.”

Ahmad Lawan an zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai a shekarar 1999 kafin ya koma majalisar dattawa, cewar Vanguard.

Ya bayyana matsalolin da ya kamata a dakile kafin kaddamar da majalisar

Ya kara da cewa, akwai wasu matsaloli da ya kamata a kawo karshensu, inda ya ce zaben shugabancin majalisar bai kamata son rai ya shiga ciki ba, sai dai duba ci gaban kasa da kuma majalisar.

Kara karanta wannan

Shugaban Ma'aikatan Tinubu: A Karshe Femi Gbajabiamila Ya Yi Martani, Ya Fadi Yadda Abun Yake

“Abin da ya kamata a duba shi ne ci gaban kasa da kuma majalisar, don haka dole a saka kowa da kowa a lamarin.
“Muna da tabbacin samun nasara, yadda Shugaban kasa a matsayinsa na tsohon sanata, da kuma mataimakinsa shi ma ya kasance a majalisar, wannan shi ne abin da kullum muke addu’an samu.”

Ahmad Lawan Ya Karyata Takarar Kujerar Majalisar Dattawa Ta 10

A wani labarin, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya karyata rade-radin cewa yana son zarcewa a shugabancin majalisar.

Lawan ya bayyana rahotannin da ke yawo akan takarar tasa a matsayin kare-rayi da yada jita-jita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.