Gwamnatin Tarayya Za Ta Sallami Wasu Sanatoci da ‘Yan Majalisa da Naira Biliyan 30
- Shugabannin majalisar tarayya za su biya makudan kudi ga ‘yan majalisar da za su bar mukamansu
- Haka zalika za a biya alawus masu tsoka ga sababbin zababbun ‘yan majalisar tarayya a Najeriya
- Ana lissafin abin da ‘yan majalisa ta tara za su batar a giratuti ya haura Naira Biliyan 30 a kasar nan
Abuja - Shugabannin majalisar tarayya sun soma aiki domin sallamar wasu da za su bar kujerunsu a yayin da ake shirin rantsar da sabuwar majalisa.
Wani rahoto da mu ka samu a Punch ya nuna makudan biliyoyin kudi za su yi ciwo wajen biyan ‘yan majalisar da suka rasa zabe hakkokin sallama.
Kilakin majalisar wakilai, Yahaya Danzaria ya shaida haka ga ‘yan majalisa a ranar Laraba.
Wa’adin Majalisar wakilan da aka rantsar a ranar 11 ga watan Yunin 2019 ya zo karshe, nan da ‘yan kwanaki ne za a rantsar da majalisa ta goma.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaban majalisar wakilai mai barin-gado, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya karanto sanarwar da ta fito daga ofishin Yahaya Danzaria a wani zama.
A tafi ofishin Akawun majalisa
"Duk wasu ‘yan majalisar tarayya za su je su karbi fam din ban-kwana domin a biya kudin giratutin sallama a ofishin Kilakin majalisa.
Kuma a dawo da shi (fam din) bayan an cike a ofishi na 2.154 or 2.031, sashen kudi da akanta zuwa ko kafin ranar Juma’a 9 ga watan Yuni."
- Rt. Hon. Femi Gbajabiamila
Punch ta ce an ware kudin da ya haura Naira biliyan 30 ga ‘yan majalisar da za su bar ofis da kuma sababbin zababbun ‘yan majalisa da jerin hadimansa.
Nawa majalisa za ta kashe?
Duka-duka, a shekarar nan ‘yan majalisar dattawa da wakilan tarayya za su kashe N194,839,144,401.
Da farko abin da gwamnatin tarayya tayi tanadi a kasafin kudin shekarar 2023 shi ne N169bn, daga baya ne ‘yan majalisa su ka kara kasonsu zuwa N194bn.
Bangare mai tsoka na kudin zai kare a sallamar wadanda ba za su koma kujerunsu ba, sai wadanda su ke zuwa majalisa a karon farko ko su ke dawowa.
Tallafin man fetur ya na cin N400bn
An ji labari shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kolo Kyari ya yi bayanin salon da Bola Tinubu ya dauka a sakamakon janye tallafin man fetur da aka yi yanzu.
Sai da ta kai a duk wata Najeriya ta na kashe Naira Biliyan 400 a wajen biyan tallafin fetur. Gwamnati ta ce kyau a kashe wadannan kudi wajen yin ayyuka.
Asali: Legit.ng