Majalisar Dokokin Jihar Filato Ta Dakatar Dukkan Ciyamomi da Kansiloli
- Majalisar dokokin jihar Filato ta fara zargin shugabannin kananan hukumomi 17, ta sanar da dakatar da su nan take a zauren majalisa
- Sabon gwamnan jihar, Caleb Mutfwang, ya amince da dakatar da Ciyamomin domin a samu damar gudanar da bincike kan zargin
- Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai taimakawa gwamna kan harkokin midiya ya fitar ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni, 2023
Plateau - Majalisar dokokin jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya ta dakatar da baki ɗaya Ciyamomi da Kansilolin kananan hukumomi 17 na jihar.
Rahoton jaridar Leadership ya tattaro cewa majalisar ta bayyana cewa matakin dakatarwa kan shugabannin kananan hukumomi da kansilolin zai fara aiki nan take.
Kakakin majalisar, Honorabul Ayuba Abok ne ya sanar da haka a zaman mambobin majalisar dokokin ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni, 2023.
Sabon gwamnan Filato ya amince da matakin
A ɓangaren zartarwa, gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya amince da dakatar da shugabannin kananan hukumomi 17 domin samun damar gudanar da gamsasshen bincike.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Babban mai taimakawa mai girma gwamna kan harkokin midiya, Gyang Bere, shi ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 2023.
Jaridar Vanguard ta rahoto sanarwan na cewa:
"Mai girma gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya karɓi takarda mai lamba S/PLHA/ADM/124/VOL.VI/XX da kwanan watan 1 ga watan Yuni daga majalisar dokoki.
"Takardan na kunshe da shawarin dakatar shugabannin kananan hukumomi 17 sakamakon gazawarsu wajen aje bayanan kuɗin shiga da waɗanda suka fita."
"Duba da wannan batu, mai girma gwamna ya amince da ɗaukar matakin dakatarwa nan take kan shugabannin kananan hukumomi da 'yan majalisarsu domin samun damar ci gaba da bincike.
Majalisar dokokin Filato ta jima tana fama da rikicin shugabanci domin ko a jiya Laraba, 31 ga watan Yuni, rahoto ya nuna jami'an 'yan sanda sun tsaurara tsaro a zauren.
Tinubu Ya Gana da Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu
A.wani rahoton na daban kuma Shugaban kasa ya gana da masu neman takarar shugabancin majalisar tarayya ta 10.
Idan baku manta ba Abbas da Kalu sun samu cikakken goyon bayan jam'iyyar APC a takarar kakaki da mataimakin kakakin majalisar wakilan tarayya ta 10.
Asali: Legit.ng