Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, Ya Sa Labule da Bola Tinubu a Villa
- Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya isa fadar shugaban kasa yanzu haka kuma ana sa ran zai gana da Tinubu
- Sabon shugaban ƙasan ya isa Villa a karon farko yau Talata, 30 ga watan Mayu, 2023 da misalin karfe 2:30 na rana
- Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima na cikin tawagar da suka tarbi shugaba Tinubu
Abuja - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa yanzu haka gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, yana cikin fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ganawa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Sabon shugaban ƙasan, wanda ayarin motocinsa suka isa Aso Villa da misalin karfe 2:30 na rana, ya tsaya kallon Faretin girmamawa da dakarun tsaron fadar suka shirya.
Tinubu ya samu tarba a Villa daga mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, Emefiele, shugaban kamfanin man Fetur, Mele Kyari, kakakin majalisar wakilai, Femi Gabajabiamila da babban sakataren Villa, Tijjani Umar.
Sauran jiga-jigan da suka tarbi Tinubu sune, tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar Legas, Wale Edun, da kuma James Faleke, zababben ɗan majalisar wakilan tarayya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Zan sake nazari kan canjin kudi - Tinubu
Idan baku manta ba, a jawabinsa na wurin bikin rantsarwa, shugaba Tinubu ya buƙaci babban bankin Najeriya ya maida hankali wajen daidaita farashin canjin kuɗi.
Haka nan ya sha alwashin sake nazari da duba kan tsarin sauya fasalin naira na tsohuwar gwamnatin Buhari, wanda CBN ya yi kokarin kakabawa 'yan Najeriya.
Tinubu ya ce:
"Ya zama wajibi CBN ya maida hankali wajen tsayar da farashin musayar kuɗi. Wannan ne kaɗai zai sauya akalar kuɗi daga hannun 'yan canji zuwa bangaren zuba hannun jarin da zai bunƙasa tattalin arzikin ƙasa."
"Ya kamata mu kara nazari kan sauya fasalin naira, a halin yanzun gwamnatina ta halasta amfani da tsoffi da sabbin takardun kuɗi."
Shugaba Tinubu ya zama shugaban Najeriya na uku da gwamnan CBN, Godwin Emefiele, zai yi aiki a karkashinsa, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Jontahan, ya fara naɗa Emefile, haka nan tsohon shugaban da ya sauka jiya, Muhammadu Buhari, ya sake sabunta naɗinsa.
Ƙotu Ta Yanke Hukunci Kan Matakin Gwamnati Na Riƙe Albashin Malaman ASUU
A wani rahoton kuma Kotun ma'aikata ta kawo karshen karar da gwamnatin tarayya ta shigar da ASUU kan tsarin ba aiki ba biyan albashi.
A cewar Kotun, tsarin rashin biyan albashi da gwamnatin tarayya ta sanya wa ASUU lokacin da take yajin aiki a shekarar da ta gabata, ya halatta kuma bata saɓa doka ba.
Asali: Legit.ng