Na Guje Wa Bikin Rantsar da Abba Gida-Gida Saboda Gudun Rikici, Ganduje

Na Guje Wa Bikin Rantsar da Abba Gida-Gida Saboda Gudun Rikici, Ganduje

  • Tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi karin haske kan dalilin da ya sa bai halarci rantsar da Abba Gida-Gida ba
  • Ya ce ya kauracewa bikin rantsuwar kama aikin sabon gwamna saboda gudun tashin rikici tsakanin magoya baya
  • Ganduje ya ce yana da yaƙini kan shugabancin Bola Tinubu kuma idan aka ba shi mukami ba zai ƙi karɓa ba

Kano - Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ya ƙauracewa bikin rantsar da sabon gwamna Abba Kabir Yusuf saboda gudun tashin rikici tsakanin magoya baya.

Da yake hira da BBC Hausa, Ganduje ya ce ba shi da wata matsala da sabuwar gwamnatin Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida na jihar Kano.

Tsohon gwamnan Kano Ganduje.
Na Guje Wa Bikin Rantsar da Abba Gida-Gida Saboda Gudun Rikici, Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Daily Trust ta rahoto Ganduje na cewa:

"Miƙa mulki ya kasu gida biyu, na farko, miƙa muhimman takardu da bayanan ayyukan gwamnati, wanda ya ƙunshi ayyukan da aka gama da waɗanda ake kan yi, da kuma bai wa sabuwar gwamnati shawarwari."

Kara karanta wannan

Zargin Kisan Kai: Abba Gida-Gida Ya Sha Alwashin Sake Gurfanar Da Doguwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na biyu shi ne bikin ranstuwa. Idan gwamnati mai barin gado da gwamnati mai zuwa suna da banbancin jam'iyya, ba dole a halarci bikin rantsuwa ba saboda gudun rikici tsakanin magoya baya."

Dagaske Ganduje yana kamun kafar neman muƙami a gwamnatin Tinubu?

Yayin da aka tambaye shi kan ko ya halarci bikin rantsar da shugaban ƙasa, Bola Tinubu, domin neman muƙami, Ganduje ya ƙara da cewa:

"Ban zo nan domin wani muƙami ba amma idan aka naɗa ni a wata kujera ba zan ƙi karɓa ba."
"Ina da kwarin guiwa a kan shugabancin Tinubu, zamu masa addu'a da goyon baya domin mutane sun zaɓe shi saboda nasarorin da ya samu a baya."

Dangane da sabanin da ake ganin akwai tsakaninsa da Abba Gida-Gida, tsohon gwamna Ganduje ya ce duk shaci faɗi ne kuma yana da kyakkyawar alaƙa da sabuwar gwamnatin Kano.

Kara karanta wannan

"Tallafin Man Fetur Ya Tafi," Shugaba Tinubu Ya Fara Ɗaukar Matakai Masu Tsauri

Jim Kaɗan Bayan Rantsuwa, Gwamna Arewa Zai Ɗauki Matasa 20,000 Aiki

A wani rahoton na daban Gwamnan Bauchi ya tabbatar da cewa gwamnatinsa zata ɗauki matasa 20,000 aikin tsaro.

A cewar mai girma gwamna, rundunar jami'an tsaron wanda ya raɗa wa suna, "hukumar 'yan banga da tallafawa matasa," suna da sumfuri iri ɗaya da na hukumar Amotekun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262