‘Mutane Sun Iya Karya’: Gwamnatin Anambra Ta Ce Ba a Wulakanta Gwamnanta a Rantsar da Tinubu Ba, Ganduje Fa?

‘Mutane Sun Iya Karya’: Gwamnatin Anambra Ta Ce Ba a Wulakanta Gwamnanta a Rantsar da Tinubu Ba, Ganduje Fa?

  • Gwamnatin jihar Anambra ta soki wani faifan bidiyo da aka gano an hana gwamnan jihar, Charles Soludo shiga wani sashen filin taron Eagle Square
  • Gwamnatin ta fitar da wata sanarwa a ranar Talata, inda ta ce an gayyaci Soludo wurin taron cikin mutuntawa don halartar bikin
  • Gwamanti har ila yau, ta bukaci mutane da su yi watsi da wannan faifan bidiyon da ke yawo da aka ce an ci mutuncin gwamnan a Abuja

FCT, Abuja – Gwamnatin jihar Anambra ta musanta wani faifan bidiyo inda aka gano an kori gwamnan jihar, Charles Soludo daga filin taro na Eagle Square da aka rantsar da Bola Tinubu da ke Abuja.

Sakataren yada labarai na gwamnan, Christian Aburime a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata 30 ga watan Mayu, ya ce an gayyaci gwamnan kamar kowa kawai dai an umarce shi ne da yaje wurin da ya dace da shi, kamar yadda tsari ya ke.

Kara karanta wannan

Tinubu: Muhimman Abubuwa 7 da Aka Tsakura Daga Jawabin Sabon Shugaban Kasa

Gwamna Charles Soludo
Gwamnatin Anambra Ta Ce Ba a Wulakanta Gwamnanta a Rantsar da Tinubu Ba, Hoto: @CCSoludo, @CAS_IOAmao.
Asali: Facebook

Ya bukaci jama'a su yi watsi da faifan bidiyon

Legit.ng ta tattaro cewa Aburime ya bayyana faifan bidiyon a matsayin aikin masu kawo cikas wadanda ba sa son zaman lafiya inda ya bukaci mutane da su yi watsi da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tattaro Aburime na cewa:

“Wannan faifan bidiyo da ya yadu a kafar sada zumunta, an kirkire shi ne don kawo rudani a cikin al’umma, kuma masu yin haka kullum burinsu shi ne su kawo bayanai na karya a cikin al’umma.
“Faifan bidiyon ya nuna yadda Gwamna Soludo ya shigo cikin Eagle Square don halartar taron rantsar da Shugaba Tinubu, sai jami’an tsaro suka nuna masa inda ya kamata ya zauna a gefen wurin zaman manyan baki.
“Nuna wa bako wurin zaman da ya dace da shi a taro ba wani matsala ba ne kuma ba kaskantar wa ba ne.”

Kara karanta wannan

Zargin Kisan Kai: Abba Gida-Gida Ya Sha Alwashin Sake Gurfanar Da Doguwa

Aburime ya ce an gayyaci Gwamna Soludo a mutunce kamar sauran gwamnoni

Ya kara da cewa:

“Gwamna Soludo ya kasance daya daga cikin gwamnoni kalilan da aka mutunta su kuma aka musu gayyata na musamman a wurin taron rantsarwar.
“Bayan haka, muna kira ga mutane da su yi watsi da wannan bidiyo da ke yawo, wannan aiki ne na masu neman kawo matsala da rudani a cikin al’umma.”

Jami’an Tsaro Sun Takawa Ganduje Burki a Wajen Rantsar da Tinubu

A wani labarin, tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya samu matsala yayin da ya sammaka zuwa wurin taron rantsar da Shugaba Bola Tinubu.

Gwamnan ya samu matsala ne a yayin da ya nufi wurin zama na manyan baki, inda daga bisani jami'an tsaro suka sauya masa wuri a gefe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.