Sabon Gwamnan Kano Ya Kori Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai, Ya Maye Gurbinsa
- Sabon gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ci gaba da korar mutanen da gwamnatin Ganduje ta naɗa
- Da safiyar Talatan nan, Gwamna Yusuf ya kori shugaban hukumar jin daɗin Alhazai ta Kano, Muhammad Abba Danbatta
- Haka nan ya rushe majalisar gudanarwan hukumar, ya sanar da sunayen sabbin mutanen da ya naɗa a muƙaman
Kano - Ƙasa da awanni 24 bayan ya karbi jagoranci, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kori shugaban hukumar jin daɗin Alhazai na jiha, Muhammad Abba Danbatta.
Mai magana da yawun sabon gwamnan, Sanusi Bature, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar da safiyar Talata, 30 ga watan Mayu, 2023, kamar yadda Punch ta rahoto.
Sanarwan ta ce Gwamna Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya amince da naɗin Alhaji Laminu Rabiu a matsayin sabon shugaban hukumar jin daɗin Alhazai ta Kano.
Haka nan sanarwan ta kara da cewa gwamnan ya kori shugaban majalisar gudanarwa na hukumar, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, wanda aka maye gurbinsa da Alhaji Yusuf Lawan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bugu da ƙari, Abba Gida-gida ya kori baki ɗaya mambobin majalisar gudanarwa ta hukumar jin daɗin Alhazai, daga cikinsu harda ɗiyar marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, Malama Nana Aisha.
Sabbin mambobin majalisar hukumar jin daɗin Alhazai
Bayan haka sanarwan ta ƙara da cewa gwamnan ya naɗa sabbin mambobin majalisar gudanarwan hukumar Alhazai ta Kano, sun haɗa da, Sheikh Abbas Abubakar Daneji da Sheikh Shehi Shehi Maihula.
Sauran mambobin su ne, Munir Lawan, Sheikh Isma’il Mangu, Hajiya Aishatu Munir Matawalle, da kuma Dakta Sani Ashir, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
A cewar sanarwar, sabbin mutanen da mai girma gwamna ya naɗa zasu karɓi iko da harkokin hukumar nan take domin tabbatar da aikin Hajjin bana 2023 ya gudana cikin nasara.
"Tallafin Mai Ya Tafi" Shugaba Tinubu Ya Fara Daukar Matakai Masu Tsauri
A wani rahoton na daban kuma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ɗauki matakin zare tallafin man fetur a Najeriya.
Tinubu, wanda ya karbi rantsuwarkama aiki ranar Litinin 29 ga watan Mayu, 2023, ya sha alwashin karkatar da kuɗin tallafin zuwa bangaren ilimi, noma da kiyo, kiyon lafiya da sauran ayyukan raya ƙasa.
Asali: Legit.ng