Gwamna Bagudu Ya Yi Sabbin Nade-Nade Masu Muhimmanci a Ranar Mika Mulki

Gwamna Bagudu Ya Yi Sabbin Nade-Nade Masu Muhimmanci a Ranar Mika Mulki

  • Gwamna mai barin gado na jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya yi sabbin nade-nade yan awanni kafin barinsa mulki
  • Bagudu ya nada sabon shugaban ma'aikata na jihar da wasu sakatarorin din-din-din guda hudu
  • A yau Litinin, 29 ga watan Mayu ne zababben gwamna, Nasiru Idris, zai karbi rantsuwa a matsayin gwamnan jihar Kebbi

Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi mai barin gado, Atiku Bagudu ya yi wasu sabbin nade-nade a ranarsa ta karshe a kan karagar mulki.

Gwamna Bagudu zai mika mulki ga zababben gwamna, Nasiru Idris nan da yan awanni kadan, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Gwamnan jihar Kebbi mai barin gado, Atiku Bagudu
Gwamna Bagudu Ya Yi Sabbin Nade-Nade Masu Muhimmanci a Ranar Mika Mulki Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Sai dai kuma, a wata sanarwa da Yahaya Sarki, hadimin labaran gwamna mai barin gado ya saki a madadin Bagudu, an nada sabon shugaban ma'aikata da wasu sakatarorin din-din-din guda hudu.

Kara karanta wannan

Tawagar Biden Ta Iso Najeriya Don Rantsar da Sabon Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu

An rahoto sanarwar na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya amince da nadin Alhaji Safiyanu Garba Bena a matsayin shugaban ma'aikatan jihar da kuma wasu sabbin sakatarorin din-din-din guda hudu.
"Sakatarorin din-din-din guda hudun sune Kudirat Shuaibu, Ibrahim Umar, Mustapha Tata da Suleiman Sani Augie
"A cewar sanarwar, nadin nasu ya fara aiki nan take."

Yana gab da mika mulki, Shugaba Buhari ya yi sabon nadi

A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sake yin sabon nadi mai muhimmanci yan awanni kadan kafin ya sauka daga kan kujerar mulki.

Shugaba Buhari a ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu, ya nada Sha'aban Sharada a matsayin shugaban hukumar kula da almajirai da yaran da basu zuwa makaranta ta kasa.

Kara karanta wannan

29 ga wata: Muhimman mukamai 3 da Tinubu zai yi bayan rantsar dashi, da wadanda zai ba

Labarin wannan nadi na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya fitar da yammacin Lahadi.

Shugabannin addinai sun gabatar da wasu bukatu a gaban Tinubu ana gab da rantsar da shi

A wani labari na daban, mun ji cewa shugabannin addinai sun fara taya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murna gabannin rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Najeriya.

Malaman addinan sun bukaci Tinubu da soke kujarun kananan minista, ya tallafawa matasa da bayar da kulawa ga bangaren ilimi da zaran ya karbi rantsuwar aiki.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel