"Zan Tafi In Bar Najeriya Fiye Da Yadda Na Same Ta a Shekarar 2015", Shugaba Buhari

"Zan Tafi In Bar Najeriya Fiye Da Yadda Na Same Ta a Shekarar 2015", Shugaba Buhari

  • Shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, ya ce zai bar mulkin ƙasar nan fiye da yadda ya sameta a shekarar 2015
  • Shugaba Buhari ya ce ya samu gamsuwa cewa ya gudanar da mulkinsa yadda ya dace sannan ya kawo ci gaba a ƙasa
  • Buhari ya buƙaci ƴan Najeriya da su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen marawa gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, baya

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa zai tafi ya bar Najeriya fiye da yadda ya sameta a shekarar 2015, lokacin da ya hau mulki.

Shugaban ƙasar mai barin gado ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja, cikin jawabin bankwana da ya aikewa ƴan Najeriya, rahoton Leadership ya tabbatar.

Shugaba Buhari ya ce zai bar Najeriya fiye da yadda ta ke a 2015
Shugaba Buhari ya ce ya kawo ci gaba a Najeriya Hoto: Channels Television
Asali: Twitter

Shugaba Buhari ya kuma nuna gamsuwa da ayyukan da ya gabatar a mulkinsa, yayin da ya ke shirin komawa Daura bayan ya miƙa mulki ga magajinsa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Yana Dab Da Sauka Mulki, Shugaba Buhari Ya Bayyana Wani Abu Da Ya Faru Da Shi Wanda Bai Taba Tunani Ba

"Ina da tabbacin cewa zan bar mulki bayan na bar Najeriya a 2023 fiye da yadda ta ke a shekarar 2015." A cewarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Buhari ya taɓa yin irin wannan kurarin na cewa ya yi mulkinsa yadda ya dace, a ranar Alhamis lokacin da ya miƙa lambobin yabo na ƙasa na Grand Commander of the Federal Republic (GCFR) da Grand Commander of the Order of the Niger (GCON) ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima.

Shugaba Buhari ya buƙaci ƴan Najeriya su marawa gwamnatin Tinubu baya

A wannan karon, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su marawa gwamnati mai kamawa baya, domin ci gaba da ɗorawa kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu.

A kalamansa:

"A yayin da zan koma gida Daura, jihar Katsina, na samu gamsuwa cewa mun fara gina sabuwar Najeriya ta hanyar ɗaukar matakan da suka dace. Sannan ina da tabbacin cewa gwamnati mai jiran gado za ta ɗora kan inda mu ka tsaya domin ganin Najeriya ta kai matsayin da ya dace da ita na babbar ƙasa."

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Ba Bola Tinubu Muhimmiyar Shawara Mai Ratsa Jiki Ana Dab Da Rantsar Da Shi

Ku Rungumi Hukuncin Da Kotu Za Ta Yi - Shugaba Buhari

A wani rahoton na daban kuma, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi kiraga ƴan adawa masu ƙalubalantar sakamakon zaɓe, da su kai zuciyoyin su nesa.

Shugaba Buhari ya buƙace su da amince da hukuncin da kotu za ta yi a kan ƙararrakin zaɓen, ko da sun yi musu daɗi ko basu yi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng