Ministoci Sun Ci Gyaran Shugaban Kasa, Sun Zargi Buhari da Sabawa Kundin Tsarin Mulki
- Ministoci sun yi zama na karshe da Muhammadu Buhari a taron FEC da aka yi a ranar Laraba
- Wasu Ministoci sun fadawa shugaban kasa doka ba ta san da zaman kujerarsu ta karamar Minista ba
- Festus Keyamo ya na da wannan ra’ayi, ya ce babu dalilin Minista ya zama karkashin wani Ministan
Abuja - Wasu Ministoci biyu da za su bar ofis sun fito sun yi ikirarin kundin tsarin mulkin Najeriya bai san da zaman wata kujerar karamar Minista ba.
Festus Keyamo SAN da Ramatu Tijjani Aliyu wadanda suke rike da mukaman kananan Minista suka fadi haka, Premium Times ta kawo rahoton.
Karamin Ministan kwadago na kasar ya shaidawa Shugaban kasa mai barin-gado cewa kujerar da suke rike da ita, ta ci karo da kundin tsarin mulki.
A jawabin karshe da ya yi a taron FEC, Festus Keyamo SAN ya ce tsarin da ake tafiya na hada Ministoci biyu a ma’aikatar tarayya guda bai aiki da kyau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun da kujerun Ministoci ba su da yawa kuma ya zama dole a nada Minista daga kowace Jiha, shugabannin Najeriya sun kirkiro karamin Minista.
Da yake jawabi a jiya, an rahoto Keyamo ya na cewa sashe na 147 na kundin tsarin mulki da ya kafa ofishin Ministan tarayya bai bambance kujerar ba.
Keyamo da Ramatu Aliyu sun koka
Ministan mai barin-gado ya ce babu bambanci wajen rantsuwa tsakanin Minista da karamin Minista, ya ce hakan tamkar a kirkiro wani sabon ofis ne.
Jaridar ta ce wannan shi ne korafin karamar Ministar harkokin birnin tarayya watau Ramatu Tijjani Aliyu, ta ce hakan ya rage masu karfi a majalisar FEC.
Duk da Ministocin gwamnatin nan sun samu damar yin aikinsu yadda ya kamata, Ramatu Aliyu ta ce maida wasu kananan Ministoci ya jawo tawaya.
Mai girma Ministar ta na ganin babu adalci a irin tsarin da ake tafiya a yanzu, duk da ta godewa gwamnati a kan damar da ta samu na yi wa kasarta aiki.
Shawarar da Keyamo ya bada shi ne a barka ma’aikatun ta yadda Minista zai zama karkashin shugaban kasa kai-tsaye a maimakon wani abokin aikinsa.
An kai Gwamnati kotu
Rahoto ya zo cewa ana karar Shugaban Najeriya da wasu Ministocinsa da kuma ofishin kula da bashi (DMO) na kasa a dalilin shirin karbo aron $800m.
Patrick Osagie Eholor zai yi shari’a da bankin Duniya da kungiyoyin cigaban kasashen waje a kotun tarayya da ke Asaba kan batun bashin da ake nema.
Asali: Legit.ng