Tirƙashi: Kansiloli a Oyo Sun Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukuma Har Sai Baba Ta Gani

Tirƙashi: Kansiloli a Oyo Sun Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukuma Har Sai Baba Ta Gani

  • Kansilolin karamar hukumar Kajola ta jihar Oyo sun dakatar da shugabansu, Afolabi Salimonu har sai baba ta gani
  • Kansilolin dai sun ce an dakatar da shugaban ne saboda yadda yake tafka kura-kurai da rikon sakainar kashi, da kuma karkatar da kuɗaɗen ƙaramar hukumar
  • Shugaban ƙaramar hukumar bai ce komai ba dangane da dakatarwar da kansilolin suka yi masa

Majalisar kansilolin ƙaramar hukumar Kajola ta jihar Oyo, ta sanar da dakatar da shugaban ƙaramar hukumar, Afolabi Salimonu, wanda aka fi sani da Borikansunwon, har zuwa abinda ya sawwaka.

Takardar dakatarwar da jaridar Punch ta samu ta bayyana cewa kansilolin sun dakatar da shugaban ne a yayin wani zama a zauren majalisar na sakatariyar ƙaramar hukumar.

Kansiloli sun dakatar da shugaban karamar hukuma a Oyo
Kansiloli sun dakatar da shugaban karamar hukuma a Oyo. Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Sun bayyana cewa matakin yana kan tsarin dokokin ƙasa da kuma dokokin majalisar jihar.

Kara karanta wannan

Tun Kafin Ya Shiga Ofis, Sarakunan Yarbawa Sun Gabatar Da Bukatunsu Ga Bola Tinubu

Dalilin dakatarwa

Kansilolin sun ce sun ɗauki wannan mataki ne sakamakon ganin yadda ake ƙara samun taɓarɓarewar abubuwa a ƙaramar hukumar saboda irin riƙon sakainar kashin da shugaban ke yi wa abubuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sannan sun zargi shugaban majalisar da karkatar da kuɗaɗe gami da yin almubazzaranci da dukiyar ƙaramar hukumar.

Sun kuma ƙara da cewar dakatarwar ta fara aikin ne nan take ba tare da wani ɓata lokaci ba, kamar yadda Inside Oyo ta wallafa.

Shugaban masu rinjaye na majalisar kansilolin, Adediran Tajudeen mai wakiltar mazaɓa ta biyu (Elero) ne ya gabatar da ƙudirin dakatarwar, a yayin da mataimakiyarsa Amusat Adebare mai wakiltar mazaɓa ta tara (Isia) ta mara masa baya.

Shugaban ƙaramar hukumar bai ce komai ba

Shugaban majalisar kansilolin, Ayegboyin Kehinde, mai wakiltar mazaba ta 8 (Isemi-Ile/Ilua)” ne ya jagoranci zaman majalisar.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Ɗalibin Jami'a a Najeriya Ya Faɗi Ya Mutu Ana Tsaka da Wasan Kwallo

Har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto, duk ƙoƙarin da aka yi na samun shugaban ƙaramar hukumar a waya ya gagara saboda baya ɗaga kiran da aka yi masa.

Shugaban ƙaramar hukuma ya lakaɗawa kansila dukan tsiya

A wani labarinmu na kwanakin baya, kun karanta yadda wani shugaban ƙaramar hukuma ya lakaɗawa ɗaya daga cikin kansilolinsa dukan tsiya a wurin taro.

Hakan dai ya samo asali ne daga wata 'yar hatsaniya da ta ɓarke a tsakaninsu kan wasu takardu da kansilolin suka buƙata daga shugaban karamar hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel