Zan Yi Duk Mai Yuwuwa Na Yi Nesa Sosai da Birnin Tarayya Abuja, Buhari

Zan Yi Duk Mai Yuwuwa Na Yi Nesa Sosai da Birnin Tarayya Abuja, Buhari

  • Shugaban ƙasa Buhari ya ce ba gudu ba ja da baya a shirinsa na nesanta kansa da birnin tarayya Abuja bayan sauka daga mulki
  • Muhammadu Buhari, ɗan asalin jihar Katsina ya ce idan mutane suka matsa masa lamba zai nemi kariya a jamhuriyar Nijar
  • A ranar Litinin 29 ga watan Mayu, 2023, ake sa ran shugaban Buhari zai miƙa wa zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu, mulkin Najeriya

Abuja - Shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, ya ƙara bayani kan shirye-shiryensa na ritaya bayan sauka daga kujerar mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Buhari ya yi ƙarin haske kan shirinsa ne a wurin kaddamar da katafariyar Hedkwatar kwastam ta ƙasa a birnin tarayya Abuja ranar Talata, kamar yadda Channels tv ta tattaro.

Shugaba Buhari.
Zan Duk Mai Yuwuwa Na Yi Nesa Sosai da Birnin Tarayya Abuja, Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shugaban Najeriya ya ce zai yi nesa sosai da birnin tarayya Abuja bayan miƙa ragamar mulki ga magajinsa, zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ranar Litini mai zuwa.

Kara karanta wannan

"Ku Koma Ofis," Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Ministoci Lokacin da Zasu Sauka Daga Mulki

A kalamansa, Buhari ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina koƙarin shirya yadda zan yi nesa matuƙa da Abuja, dama na fito daga gari mai nisa daga birnin tarayya Abuja."

Idan yan Najeriya suka matsa mun zan koma Nijar - Buhari

A cewar Shugaba Buhari, idan 'yan Najeriya suka ƙuntatawa rayuwarsa bayan sauka daga mulki, jamhuriyar Nijar a shirye take ta ba shi matsuguni da kariya.

Punch ta rahoto shugaba Buhari na cewa:

"Ina faɗin wannan batutuwan da suka shafi rayuwata ne saboda kwana shida kacal suka rage mun. Na gaya muku duk wanda ya matsa mun, ina da dangantaka mai kwari da makotanmu, mutanen Nijar zasu kare ni."

Bayan haka, Muhammadu Buhari, ya ce yana sane za'a wahala amma ya garƙame iyakokin Najeriya domin habaƙa samar da kayan abinci a cikin gida.

Duk da yan Najeriya sun ta sukar yunkurin gwamnatin tarayya, Buhari ya ce daga baya mutane sun fahimta kuma sun gode masa.

Kara karanta wannan

"Na Yafe Maka": Gwamnan Arewa Ya Aike Da Sako Mai Girma Ga Shugaba Buhari

Zan Iya Komawa Ɗan Jarida Mai Zaman Kansa Bayan Na Sauka Mulki, Ortom

A wani rahoton na daban kuma Gwamna Ortom ya ce idan ya so, zai koma ɗan jarida bayan ya sauka daga kan mulki ranar 29 ga watan Mayu.

Ortom, gwamnan jihar Benuwai a inuwar jam'iyyar PDP, ya ce yana da zabi cikin abu uku da zai runguma bayan mulkinsa ya ƙare ranar Litinin mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262