Zan Iya Komawa Ɗan Jarida Mai Zaman Kansa Bayan Na Sauka Mulki, Ortom
- Gwamna Ortom ya bayyana ayyuka 2 da zai iya komawa bayan sauka daga mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2023
- Ortom na shirin karkare zangon mulki na biyu a matsayin gwamnan jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya
- Yana ɗaya daga cikin gwamnonin da suka yi yunkurin ritaya a majalisar dattawa, amma tsohon hadiminsa ya kawo masa cikas
Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya ce mai yuwuwa ya koma ɗan jarida bayan ya sauka daga kan kujerar gwamma ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
Ortom, wanda zangon mulkinsa na biyu ke dab da ƙarewa, ya sha kashi a zaben Sanatan Benuwai ta Arewa maso Yamma a hannun tsohon hadiminsa na jam'iyar APC.
Da yake hira da Arise TV game da shirinsa na gaba bayan ya sauka daga mulki, Ortom ya zargi fadar shugaban ƙasa da amfani da kuɗi don tabbatar da ya sha kaye a zaben da ya wuce.
Ya ce akwai abubuwa da dama da zai iya runguma bayan wa'adin mulkinsa ya ƙare a karshen watan Mayu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daily Trust ta rahoto gwamna Ortom na cewa:
"Na san adadin zunzurutun kuɗin da fadar shugaban ƙasa ta tunkuɗo jihar Benuwai don kawai a ga baya na a zaɓe, bakomai na saduda kuma zan goyi bayan duk wanda ya buƙaci na mara masa baya."
"Amma idan ba su buƙatar taimako na, zan koma gonata, zan koma na rungumi kasuwanci na, kai zan ma iya komawa na kama aikin jarida."
Buhari ya maida Najeriya baya - Ortom
Gwamna Ortom ya ƙara cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta maida hannun agogo baya a Najeriya amma duk da haka ya yafe wa shugaban ƙasan laifin da ya masa.
Bugu da ƙari, Ortom ya yi fatan samun canji a gwamnatin zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wanda zai kama aiki nan da 'yan kwanaki.
"Na Yafe Maka," Gwamnan Arewa Ya Aike Da Sako Mai Girma Ga Shugaba Buhari
A wani labarin kuma Gwamna Samuel Ortom, ya yafe wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kuma ya ba shi shawara.
Gwamnan wanda ke takun saƙa da musayar yawu da fadar shugaban ƙasa kan kashe-kashen da ke aukuwa a jihar Benuwai, ya ce Addinin kirista ya koya musu a yafe wa juna.
Asali: Legit.ng