Abin Da Ya Sa Jamhuriyar Nijar Za Ta Kare Ni Idan Aka Matsa Min Bayan Na Sauka Daga Mulki, Buhari

Abin Da Ya Sa Jamhuriyar Nijar Za Ta Kare Ni Idan Aka Matsa Min Bayan Na Sauka Daga Mulki, Buhari

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yana da kyakyawar alaƙa da jamhuriyar Nijar kuma za su kare shi idan ‘yan Najeriya suka takura masa bayan ya bar mulki
  • Buhari ya kuma ce yana shirin komawa mahaifarsa Daura, wacce ta ke nesa da Abuja kuma kusa da jamhuriyar Nijar
  • Buhari ya kuma ce da gangan ya naɗa mata a matsayin ministocin kuɗi a shekaru takwas da ya yi ya na mulki saboda maganin masu zuwa neman alfarma

Abuja - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya jaddada irin kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsa da maƙwabciyar kasar Najeriya wato jamhuriyar Nijar.

Buhari, wanda wa’adin mulkinsa ke ƙarewa cikin 'yan kwanakin nan, ya yi bayanin irin kyakkyawar alaƙar da ya ke da ita da ƙasar.

Buhari ya ce in aka takura masa zai koma Nijar
Buhari ya ce zai koma Nijar in aka takura masa bayan sauka daga mulki. Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Nijar za ta kawo min ɗauki in aka takura min

Kara karanta wannan

"Na Yafe Maka": Gwamnan Arewa Ya Aike Da Sako Mai Girma Ga Shugaba Buhari

Ya ce idan ‘yan Najeriya suka takurawa ƙasar bayan bikin miƙa mulki da za a yi a ranar 29 ga watan Mayu, Nijar za ta kawo masa ɗauki, in ji rahoton The Punch.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin ƙaddamar da hedikwatar hukumar kwastam ta ƙasa ta N19.6bn a Abuja, ranar Talata.

A yayin da ya ke jawabi a wajen bikin kaddamarwar, Buhari ya kuma bayyana cewa yana shirin komawa mahaifarsa Daura, wacce take nesa da Abuja, kuma kusa da jamhuriyar Nijar.

Ya ce:

“Ina faɗar waɗannan abubuwan da suka shafe ni ne saboda saura kwanaki shida na sauka.”
“Kuma ina ƙoƙarin yin nesa da Abuja yadda ya kamata. Dama na fito ne daga wani yanki da ke nesa da Abuja.”
"Sannan idan wani ya cika takuramin, ina da kyakkyawar alaƙa da makwabtana. Mutanen Nijar za su kare ni.”

Kara karanta wannan

Daga Karshe Shugaba Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Ya Garkame Iyakokin Kasar Nan

A cewarsa, idan mutum ya kasa samun kyakkyawar alaƙa da maƙwabcinsa, to ɗansa ko jikansa za su iya fuskantar ƙalubale a gaba.

Da gangan na naɗa mata ministocin kuɗi

Buhari ya kuma bayyana cewa da gangan ya naɗa mata a matsayin ministocin kuɗi, a cikin shekaru takwas da ya yi yana mulki domin yaƙar waɗanae ke kawo cikas ta hanyar zuwa neman alfarma.

Buhari ya ce mafi yawan maza ba za su iya zuwa neman alfarma wajen mace da ke a matsayin ministar kudi ba.

Su waye ministocin kudin Buhari?

Ministar kuɗin Buhari ta farko ita ce Misis Kemi Adeosun, wacce ta yi murabus saboda badaƙalar NYSC a shekarar 2017.

Bayan murabus din Adeosun, shugaba Buhari ya naɗa Misis Zainab Ahmed ta shugabanci ma’aikatar ta kuɗi.

A rahoton Vanguard, Buhari ya kuma bayyana cewa ya kulle iyakokin ƙasar nan ne saboda 'yan ƙasa su dage wajen noma abinda za a ci.

Kara karanta wannan

"Ta Ciri Tuta": Kyakkyawar Bahaushiya 'Yar Najeriya Ta Zama Soja a Amurka, Bidiyonta Ya Yadu Sosai

Buhari ya nemi alfarmar Tinubu

A labarinmu na baya, mun kawo muku cewa shugaba Buhari mai barin gado, ya roki zababben shugaban kasa Bola Tinubu da ya ci-gaba da mutunta ma'aikatan gwamnatin kasa.

Ya bayyana hakan ne a wajen bikin zagayowar ranar ma'aikata ta duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng