Manyan Abubuwa 7 Da Suka Faru Tsakanin 2019 Da 2023 a Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya

Manyan Abubuwa 7 Da Suka Faru Tsakanin 2019 Da 2023 a Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya

  • Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya jagoranci Majalisa ta tara daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa yau
  • ‘Yan majalisar wakilan tarayyar sun kawo kudirori fiye da 2, 000 wanda an amince da wasu a cikinsu
  • A lokacin Gbajabiamila ne kudirin PIA da CAMA suka zama doka, kuma an canza dokar zabe

FCT, Abuja - Yayin da wa’adin Femi Gbajabiamila ya ke zuwa karshe a majalisa, Daily Trust ta tattaro abubuwan da suka faru a majalisar wakilan tarayya.

1. Wasu bangarori 10

An nada kwamiti da ya tsara ayyukan da ‘yan majalisa za su yi domin kawo tsare-tsare da za su taimakawa gwamnati a wasu muhimman bangarori 10.

Jaridar ta ce bangarorin su ne kiwon lafiya, ilmi, tattalin arziki, tsaro, noma, wuta, sauyin yanayi, sai kuma cigaban al’umma, walwala da harkar gidaje.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Buhari ya Ware N15bn a 2023 Don Kare Dalibai, Cewar Zainab Ahmed

Femi Gbajabiamila
Femi Gbajabiamila a Majalisar Wakilan Tarayya Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

2. Sha’anin Tsaro

Majalisa ta tara ta maida hankali a kan sha’anin tsaro har sai da ta kai an matsawa shugaban kasa lamba cewa ya canza hafsoshin sojoji da ake da su a Najeriya.

3. Kawo Dokoki a Kasa

Daga 2019 zuwa watan Maris a 2023, majalisar wakilai ta kawo kudirori 2, 209 wanda daga ciki aka amince da 451, hakan ya sa sun sha gaban kowace majalisa.

4. Fitattun Kudirori

Akwai kudirorin da suka yi fice a cikin wadanda aka amince da su. Jaridar ta ce a cikinsu akwai PIA, kudirin zabe da kudirin CAMA da duk sun zama dokoki.

Akwai kudirorin da suka maida hankali a kan tattaln arziki, tituna, sauyin yanayi da ire-irensu.

5. Tsoma Baki Kan Rikicin Kungiyoyi

‘Yan majalisa a karkashin Gbajabiamila sun tsoma baki domin shawo kan sabanin gwamnati da kungiyoyi kamar NARD ta likitoci da malaman jami’a na ASUU.

Kara karanta wannan

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Sa Hannu, Ya Kawo Dokoki 8 a Makon Karshensa a Ofis

6. Rikicin Sudan

Kamar yadda majalisa ta shawo kan ASUU da NARD, an tura tawaga karkashin Alhassan Ado-Doguwa domin ganin an ceto ‘Yan Najeriya daga kasar Sudan.

7. Canjin Kudi

Majalisar wakilan tarayya ta gayyato Gwamnan bankin CBN ta nemi a dakatar da tsarin canjin kudi, ta ce sauyin da aka zo da shi ya jefa al’umma cikin kuncin.

An kori Shugaban NAMA

Ku na da labari Tayib Adetunji Odunowo ya maye gurbin Matthew Pwajok wanda aka kora daga NAMA a zazzagar da gwamnati ta ke yi a ma’aikatar jirgin sama.

Ganin ‘Yan kwanaki kadan da suka wuce Hadi Sirika ya sallami Shugaban Hukumar FAAN, Ministan ya ce bai da wata boyayyar manufa, ya ce wa'adi ne ya cika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng