Gwamnoni 5 Masu Barin Gado Wadanda Mai Yiwuwa Ba Za Su Miƙa Mulki Cikin Ruwan Sanyi Ba Da Dalilai
Gabanin ranar 29 ga watan Mayu da wa'adinsu zai ƙare a hukumance, ana sa ran miƙa mulki ga waɗanda za su gaje su kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Sai dai saboda wasu dalilai, wasu daga cikin gwamnoni masu barin gado, ba dole ne su yi abin da ya kamata ba wajen miƙa mulkin.
Domin kuwa ana zargin waɗannan gwamnoni da ƙin bai wa kwamitocin amsar mulki na zaɓaɓɓun gwamnonin jiharsu haɗin kai.
Takun-saka tsakanin kwamitocin miƙa mulkin da gwamnoni masu barin gado, ya samo asali ne daga tambayoyi kan halin da kuɗin jihohin ke ciki da kwamitocin ke yi.
Ga dai jerin sunayen gwamnonin biyar masu barin gado da suka shiga cikin wannan rukuni:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bello Matawalle
Ana zargin gwamnan jihar Zamfara da ƙin bayar da haɗin kai ga kwamitin da Dauda Lawal Dare ya kafa, gabanin ƙaddamar da gwamnatin PDP a jihar a ranar 29 ga watan Mayu.
Rahotanni sun bayyana cewa, Dauda Dare ya kafa wani kwamiti da zai binciki yadda aka kashe kuɗaɗen ma’aikatun jihar, hukumomin bada tallafi masu zaman kansu (MDAs), matakin da gwamnatin jihar ta yi watsi da shi.
Samuel Ortom
Gwamnan jihar Benuwai ma dai ba ya ga-maciji da zaɓaɓɓen gwamna Rabaran Hyacinth Alia na jam'iyyar APC. Kwamitocin miƙa mulki da bangarorin biyu suka kafa sun kasance cikin cece-kuce.
Kwanannan aka jiyo Ortom ya yi alƙawarin miƙa wa Alia a ranar 28 ga Mayu, kwana guda gabanin ranar da kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada don miƙa mulki.
Abdullahi Ganduje
Kwamitin miƙa mulki da sabuwar jam’iyya mai kayan marmari (NNPP) ta kafa a Kano, ya zargi gwamna mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje da rashin bayar da haɗin kai.
Kwamitin wanda ke ƙarƙashin shugabancin Abdullahi Bappa Bichi, ya bayyana cewa sai bayan wani taron manema labarai ne suka fara samun haɗin kan gwamnan, amma duk da haka ba kamar yadda ake tsammani ba.
Okezie Ikpeazu
Ana zargin gwamnan jihar Abia mai barin gado shi ma da ƙin bayar da haɗin kai ga kwamitin da zaɓaɓɓen gwamnan, Alex Otti ya kafa.
Mambobin kwamitin na Otti sun yi ƙorafin cewa ayyukansu ka iya samun tasgaro, saboda jinkirin fitar da takardar miƙa mulki.
Simon Lalong
Shugaban kwamitin miƙa mulki na jihar Filato, ya ce shirin miƙa mulki na nan lafiya lau, amma ƙaramin shugaban kwamitin ya bayyana akasin haka, in ji rahoton The Punch.
Yiljap Abraham, shugaban kwamitin watsa labarai ya yi zargin cewa gwamnatin Lalong mai barin gado ba ta fitar da kuɗaɗe isassu ba don shirye-shiryen bikin miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Gwamnan APC ya zama shugaban gwamnonin arewa
A wani labarin na daban, kun ji cewa gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya yi nasarar zama sabon shugaban kungiyar gwamnonin arewa.
Gwamna Simong Lalong na jihar Filato ne dai ya sauka daga shugabancin kungiyar gwamnonin na arewa.
Asali: Legit.ng