Sanata Sani Musa Ya Nesanta Kansa Da Shirin Dawo Da Ahmed Lawan a Matsayin Shugaban Majalisa Dattawa
- Sanatan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya bayyana gaskiya dangane da ƙulla-ƙullar da ake yi kan Ahmed Lawan
- Sanata Mohammmed Sani Musa daga jihar Niger, ya bayyana cewa baya da wata masaniya kan zargin da ake masa na goyawa Ahmed Lawan baya ya yi tazarce
- Sanatan ya yi bayanin cewa yana nan daram akan matsayar da takwarorinsa na yankin Arewa ta tsakiya suka cimma, na ganin ya zama mataimakin shugaban majalisa
Abuja - Sanata Mohammad Sani Musa, sanata mai wakiltar Niger ta Gabas a majalisar dattawa, ya nesanta kansa daga zargin cewa da shi da wasu zaɓaɓɓun sanatoci suna kitsa yadda Ahmed Lawan, zai sake zama shugaban majalisar dattawa ta 10.
Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa, a wata sanarwa da sanatan wanda ya ke neman mataimakin shugaban majalisar ya fitar ranar Litinin, ya ce rahoton wannan shirin ƙoƙarin kawai kawo ruɗani ne a tsakanin jam'iyyar APC da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Tribune tace sanatan ya bayyana cewa wannan iƙirarin da ake yi kawai zuƙi ta malle ce, inda ya ƙara da cewa yana nan akan matsayar da takwarorinsa na yankin Arewa ta tsakiya, suka cimma na mara masa baya ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawan.
A kalamansa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ba zanyi wani abu da ya saɓawa matsayar da takwarorina suka cimmawa ba wacce gwamnonin yankin Arewa ta tsakiya suka amince da ita."
"Babu wani taron da aka yi, inda aka yi jarjejeniya da ni da sauran zaɓaɓɓun sanatoci domin goyon bayan Ahmed Lawan da Osita Izunaso, su zama shugaba da mataimakin shugaba na majalisar dattawa ta 10."
Jam'iyyar APC mai mulki dai tuni ta zaɓi sanata Godswill Akpabio, tsohon ministan harkokin Niger Delta, a matsayin shugaban majalisar dattawa, da sanata Barau Jibrin, sanata mai wakitar Kano ta Arewa a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa.
Ahmad Lawan Zai Iya Shiga Takarar Majalisar Dattawa
Rahoto ya zo cewa Sanata Ahmed Lawan, na shirin kawo wani sabon ruɗani a takarar shugabancin majalisar dattawa ta 10.
Shugaban majalisar dai yana shirin shiga cikin tseren neman kujerar shugabancin majalisar dattawa ta 10.
Asali: Legit.ng