Kotu Ta Yi Watsi da Karar Jam'iyyar APC Kan Zaben Gwamnan Rivers
- Kotun sauraron ƙarar zaben gwamna a jihar Ribas ta kori ƙarar da jam'iyyar APC ta kalubalanci nasarar PDP a babban zaben 2023
- An ɗanyi sa'insa tsakanin lauyoyin jam'iyyar APC gabanin Alkali ya yanke korar karar nan take ranar Litinin 22 ga watan Mayu
- Lauyan APC ne ya fara neman Kotu ta sallami ƙarar, daga bisali Alkali ya amince da bukatar, ya tatattaki ƙarar APC
Rivers - Kotun sauraron ƙorafin zaben gwamna a jihar Ribas ta kori ƙarar da jam'iyyar APC ta shigar tana kalubalantar nasarar jam'iyyar PDP a babban zaben da ya wuce.
Rahoton Channels tv ya nuna cewa sakamakon janyewar APC, ya rage sauran ɗan takarar gwamna a inuwar APC, Tonye Cole, a ɓangaren masu ƙara.
Mista Cole ya kalubalanci jam'iyyar PDP, zababben gwamnan jihar Ribas, Simi Fubara, da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).
Cole ya garzaya Kotun zaɓem jiha yana kalulantar matakin INEC na ayyana ɗan taƙarar PDP, Mista Fubara, a matsayin zababben gwamnan jihar Ribas bayan kammala zaɓe.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda aka yi jayayya a gaban Kotu
Bayanai sun nuna an buga dirama a gaban Kotun, lokacin da jam'iyyar APC ta roƙi Kotu damar canja lauyan da zai fafata a ƙasar domin kalubalantar Fubara da PDP.
Tun a farkon fara sauraron karar yau Litinin, Lauyan APC Solomon Umoh, ya sanar da Kotu cewa shi ne zai jagoranci lauyoyin da zasu tsayawa APC har ƙarshen shari'ar.
Umoh, ya kuma faɗa wa Kotu cewa jam'iyyar da yake karewa tana rokon Kotu ta zare sunanta daga cikin jirin masu ƙara, kana ta yi fatali da karar baki ɗaya.
A nasa bangaren tsohon Lauyan APC ya ce sam ba shi da labarin cewa wanda yake wa aiki ta canja sabon lauya, kamar yadda Sanara Reportera ta ruwaito.
Kotu ta yanke hukunci nan take
Kwamitin alkalai uku ta bakin mai shari'a Cletus Emifoniye, ya aminta da bukatar APC na sauya lauya kana ya kori jam'iyyar daga cikin jerin masu ƙara a shari'ar.
PDP ta fara shiga matsala a Kogi
A wani labarin kuma ɗan takara PDP a zaben gwamnan jihar Kogi ya shiga tsaka mai wuya tun gabanin gudanar da zaben a watan Nuwamba.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamna Yahaya Bello, ya kara naƙasa PDP, ya tarbi manyan jiga-jigai da tsoffin shugabanni zuwa jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng