PDP Ta Fara Tangal-Tangal, Tsohon Shugaban Jam'iyya da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma APC
- Gwamna Yahaya Bello ya karbi dandazon mambobin PDP da suka sauya sheƙa zuwa.APC a karamar hukumar Igalamela/Odolu jihar Kogi
- Wannan lamarin babbar barazana ce ga Sanata Dino Melaye, ɗan takarar gwamna a inuwar PDP a zaben da ke tafe a watan Nuwamba
- Abdullahi Ibramin, tsohon shugaban rikon kwarya a karamar hukumar da wasu manyan jiga-jigai na cikin masu sauya sheƙar ranar Litinin
Kogi - Ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PDP a zaben jihar Kogi da ke tafe, Sanata Dino Melaye, na fuskantar babbar barazana gabanin zaben wanda zai gudana a watan Nuwamba, 2023.
Wannan na zuwa ne yayin da gwamnan jihar, Yahaya Bello, ya tarbi tawagar gungun mambobin PDP daga ƙaramar hukumar Igalamela/Odolu zuwa cikin jam'iyar APC ranar Litinin 22 ga watan Mayu.
Meyasa jiga-jigan PDP suka zabi shiga APC?
Masu sauya sheƙar sun sha alwashin goyon bayan ɗan takarar gwamna a inuwar APC mai mulki, Ahmed Usman Ododo, kamar yadda jaridar Tribune Online ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Haka nan sun bayyana cewa zasu yi aiki tuƙuru ba dare ba rana domin tabbatar da APC ta ci gaba da mulkin jihar Kogi.
Tsohon shugaban PDP na rikon kwarya a karamar hukumar Igalamela/Odolu, tare da Honorabul Adama Sani da Aikoye Anu ne suka jagoranci masu sauya shekar daga gundumar Ajaka 1 da 2 zuwa APC.
Gwamna Bello ya zuba aiki a Kogi
A madadin tawagar masu sauya shekar, Ibrahim ya ce ayyukan Alherin da gwamna Bello ya zuba wa talakawa a kananan hukumomin Kogi ne suka ja hankalinsu zuwa APC.
Tsohon jigon APCn ya ambato sabunta titin Umomi-Akpagidigbo-Ugwolawo-Ajaka-Idah da wasu manyan ayyukan gwamnan a matsayin musabbanin sauya sheƙarsu.
Ya ƙara da cewa nasarorin da gwamnatin Yahaya Bello ta samu sun ja hankalin mambobin PDP, ba wai su kaɗai ba, sun koma jam'iyyar APC mai nasara, kamar yadda Guardian ta ruwaito.
Gwamna El-Rufa'i Ya Tsige Sarakuna 2 da Hakimai Uku
A wani rahoton na daban, Gwamna El-Rufai ya Sauke Sarakuna 2 daga kan karagar mulki a Kaduna, ya tsige Hakimai 3.
A wata sanarwa ɗa kwamishinar kananan hukumomi ta fitar ranar Litinin, gwamnan ya bayyana manyan dalilansa na tuɓe rawanin Sarakunan.
Wannan mataki ya zo ne yayin da ya rage mako ɗaya tal El-Rufai ya sauka daga mulki ya miƙa wa zababben gwamna, Malam Uba Sani.
Asali: Legit.ng