Primate Ayodele Ya Hango Wani Mummunan Abu Da Zai Faru a Mulkin Tinubu
- Wani malamin addini a Najeriya ya yi wani hangen nesa mai ban tsoro dangane da gwamnati mai jiran gado ta Bola Tinubu
- Primate Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa za a samu rigingimu a tsakanin manyan ƙusoshin cikin gwamnati da magadansu
- A cewar faston, cigaban wasu jihohi da ƙasar nan zai samu tawaya a dalilin rikicin da zai ɓarke tsakanin manyan ƴan siyasa a gwamnatin Tinubu
Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana abinda zai faru da gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Babban faston ya yi nuni da cewa wasu daga cikin zaɓaɓɓun ƴan siyasar da aka zaɓa, za su yi rikici da waɗanda suka gada daga kan mulki, a matakin jiha da na tarayya, cewar rahoton Daily Independent.
A wata sanarwa da hadiminsa kan watsa labarai, Osho Oluwatosin, ya fitar, Primate Ayodele, ya yi nuni da cewa gwamnati mai kamawa za ta samu ruɗani sosai wanda zai kawo rabuwar kai a tsakanin ƴan siyasa.
Ya yi ƙarin haske cewa hakan zai shafi ƙasar nan da wasu jihohi, saboda cigaban su zai samu tawaya a dalilin rikicin da ƴan siyasar za su yi, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Wannan gwamnatin mai jiran gado za ta fuskanci rikice-rikice a matakin jihohi da tarayya. Wasu daga cikin magada za su yi faɗa da waɗanda suka gabace su kan mulki, saboda za su ga abubuwan da ba su yi tsammani ba."
"Wasu za su yi faɗa kan butulci da rashin biyayya, za a samu rikici sosai a ƙasar nan a dalilin rarrabuwar kawuna a tsakanin masu riƙe da madafun iko."
Ƴan siyasar da za su yi faɗa da magadansu
Ya yi nuni da cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai samu matsala da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, gwamna Wike na jihar Rivers, zai yi rikici da magajinsa Sim Fubara, haka gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa da magajinsa, Sheriff Oborevwori, da sauran su.
"Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno da Emmanuel Udom za su samu rikici sosai a gwamnati mai kamawa. Gwamna Okowa da gwamna mai jiran gado na jihar Delta, Sheriff Oborevwori, za su zama maƙiyan juna." A cewarsa.
Primate Ayodele Ya Ce Ana Iya Tsige Gwamnoni Uku
A baya rahoto ya zo kan yadda Primate Ayodele ya hango wasu gwamnoni uku waɗanda za a iya ƙwace nasarar da suka samu a zaɓen 2023.
Babban faston ya hasaso cewa nasarar Uba Sani a jihar Kaduna ba tabbatacciya bace, domin mulki na iya komawa hannun ɗan takarar PDP, Isah Ashiru Kudan.
Asali: Legit.ng