Kotun Zaben Shugaban Kasa: Abin Da Ya Sa Kotu Ta 'Sauke' Karar Obi Kan Tinubu: KAI TSAYE

Kotun Zaben Shugaban Kasa: Abin Da Ya Sa Kotu Ta 'Sauke' Karar Obi Kan Tinubu: KAI TSAYE

A ranar Litinin 8 ga watan Mayu ne Kotun Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa ta fara sauraron korafin kan zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Wannan lamari na da matukar muhimmanci saboda shine zai iya nuna makomar rikici da ake yi kan sakamakon zaben.

Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Tinubu da Peter Obi suna fafatawa a kotun zaben shugaban kasa
An fara sauraron kara a kotun zaben shugaban kasa a Abuja. Hoto: KOLA SULAIMON/AFP, PATRICK MEINHARDT/AFP, PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Asali: Getty Images

Ku kasance tare da Legit.ng Hausa don samun bayanai dangane da zaman Kotun Sauraron Zaben Shugaban Kasar.

Ranar 2 ga Watan Yuni: Bayanai Kai Tsaye Daga Kotun Sauraron Zaben Shugaban Kasa

A yau Juma'a 2 ga watan Yuni kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa da cigaba da zamanta.

Ana sa ran kotun za ta cigaba da duba hujojin da jam'iyyar Labour da dan takararta suka gabatar na kallubalantar nasarar Shugaba Bola Tinubu.

Hakazalika, kotun za ta duba karar da jam'iyyar APM ita ma ta shigar.

Kotu ta cigaba da zamanta

Bayan wani dan lokaci, kotun ta dawo domin cigaba da zamanta biyo bayan umurtar lauyoyin Obi su shirya takardunsu bisa tsari kafin fara shari'ar.

Bisa alamu lauyoyin ba su shirya yadda ya dace ba, hakan yasa alkalan kotun suka nuna cewa akwai alama lauyoyin na Obi ba su fahimci sarkakiyar da ke tattare da aikin da aka ba su ba.

Domin kada a bata lokaci, alkalan biyar sun shawarci Emeka Okpoko, jagoran lauyoyin Obi ya tabbatar ya shirya takardunsa kafin ya gabatar da su. Sun ce a dena daukar kotun tamkar kasuwa.

Amma, wani lauya cikin tawagar, Awa Kalu, ya yi magana ya sanar da kotun cewa sun nemi a daga karar zuwa yau ne domin su dauki mataki kan wasu muhimman abubuwa. Ya ce ba su shirya zuwa gida ba kuma za su so su cigaba da gabatar da takardun a gaban kotun. Kalu ya nemi a karbi takardun kananan hukumomi 16 cikin 21 na Jihar Rivers.

A martaninsa, Mai Shari'a Haruna Tsamani ya yarda a karbi takardun da aka shirya su yadda ya dace.

Kotu ta dakatar da karar Peter Obi kan Tinubu na tsawon mintuna 10

Kotun sauraron karar shugaban kasar ta dakatar karar da Obi da Jam'iyyar Labour suka shigar kan Bola Tinubu na tsawon mintuna 10.

An jingine karar ne saboda rashin daidaita takardun da aka gabatarwa kotun a matsayin hujja na yin magudi yayin zaben shugaban kasar.

A yayin da aka zauna don cigaba da sauraron karar, kotun ta gano cewa ba a shirya takardun ba kamar yadda ta umurta.

An gano wasu matsaloli yayin duba takardun kananan hukumomi 23 na Jihar Benue.

Lauyan Obi da jam'iyyar Labour, Emeka Okpoko ya nemi amfani da wasu takardu da a baya bai sanar da kotun da su ba, amma an ki amincewa da hakan don ya saba doka.

Daga bisani kotun ta dakatar da sauraron karar na mintuna 10 ta umurci lauyoyin su sake shirya takardun bisa tsarin da aka amince da shi kafin fara shari'ar.

Ranar 1 ga Watan Yuni: Bayanai Kai Tsaye Daga Kotun Sauraron Karar Zaben Shugaban Kasa

Kotun ta cigaba da sauraron karar da Jam'iyyar Labour da Peter Obi suka shigar na kallubalantar nasarar Shugaba Bola Tinubu.

A yau Alhamis 1 ga watan Yunin ma Peter Obi da mataimakinsa Datti Baba-Ahmed, sun halarci zaman kotun.

PDP, Atiku sun fara gabatar da kararsu, sun bada takardu da aka fitar daga BVAS, sakamakon zabe, wasu

A bangare guda, PDP kuma ta ba wa kotun ainihin kwafin sakamakon zabe, takardu daga na'urar BVAS, da bayanai na katin masu zabe da aka tattaro daga jihohi 36 da Abuja.

An bada takardun ne gabanin fara sauraron karar da PDP da Atiku suka shigar.

An karbi takardun da lauyan mai kara, Eyitayo Jegede (SAN) ya gabatar an ajiye su a matsayin hujja, duk da cewa lauyan wanda aka yi karar sun nuna rashin yarda da wasu cikinsu.

Masu karar ba su kira shaidu ba a yanzu.

Shaidan Peter Obi ya farko ya magantu a kotu

Bayan kotun ta karbi takardun a matsayin hujja, Okutepa ya kira shaidansa na farko.

Shaidan, Lawrence Nwakaeti, ya ce ya bada ba'asinsa kan batun a ranar 20 ga watan Maris a kotun Abuja.

Nwakaeti, lauya, ya fada wa kotun cewa ya yi zabe a ranar 25 ga watan Fabrairu a rumfar zabe ta Umuezeala Village Square, Ihiala, Jihar Anambra.

Nwakaeti ya ce kotun Amurka ta ci Tinubu tara saboda safarar miyagun kwayoyi.

Amma yayin lauyan Tinubu, Wole Olanipekun ke masa tambaya, Nwakaeti zai yi mamaki idan aka fahimtar da shi cewa ba a ci tarar Tinubu ba a cikin takardun da ya gabatarwa kotu.

Da aka masa tambaya ko ya taba zuwa Amurka, Nwakaeti, ya sam cewa eh.

Ya ce ya ziyarci Michigan a 2003.

Kuma, lauyan APC, Lateef Fagbemi (SAN) ya tambayi Nwakaeti ko ya san a hukumance a bada rahoton wanke Tinubu daga hannun jami'in shari'a na ofishin jakadancin Amurka, da ke nuna Tinubu bai yi wani laifi ba.

A amsarsa, Nwakaeti, ya ce bai san an bada rahoton wanke Tinubu ba.

Bayan shaidan ya kammala bada ba'asinsa, kotun ta dage zamanta zuwa ranar Laraba don cigaba da shari'a.

Kotun ta karba takardu na zargin cewa an samu Tinubu da aikata laifuka masu alaka da miyagun kwayoyi

Kotun ta karbi takardu a matsayin hujja da ke zargin Shugaba Tinubu da laifukan miyagun kwayoyi a Amurka.

Lauyan Peter Obi, Jibrin Okutepa (SAN) ya mika wa kotun wasu takardu da ya ke ikirarin cewa kotun ta ci Tinubu tarar $460,000 saboda safarar miyagun kwayoyi a Northern District of Illinois, Eastern Division.

Karar mai lamba: 93C 4483 tsakanin Amurka ne da Tinubu.

Okutepa kuma ya gabatar da takardu don taimakawa shari'ar zargin takara biyu da aka ce Kashim Shettima ya yi.

INEC ta magantu kan takardun da jam'iyyar Labour ta gabatar

INEC ta bakin lauyanta Abubakar Mahmoud ta ce ba daidai bane a rika boye wa INEC bayanai dangane da takardun da wanda ya yi kararsu zai gabatar.

Don haka ya kira abin da LP ke son yi a matsayin shari'a 'ta hanyar mamaya' domin ba a riga an basu takardun da za a gabatar ba.

Mahmoud ya kara da cewa yana da muhimmanci INEC ta tabbatar da sahihancin takardar.

Kotun ta amince da abin da lauyan INEC ya ce tana mai cewa ya kamata INEC ta ga takardun.

Kotun ta tafi hutun minti 10 don a warware batun.

Jam'iyyar Labour ta shirya gabatar da shaidarta na farko

Jam'iyyar Labour ta ce ta shirya don gabatar da shaidarta na farko. Peter Obi, wanda lauyansa Jibril Okutepa ke wakilta a kotun ya ce za su mika wa kotu wasu takardu kafin shaidan ya bada bahasinsa.

Takarda na farko da za su bayar ita ce form EC11A, mai kwanan wata 14 ga watan Yulin 2022. Wannan fom din na dauke da sa hannun Kashim Shettima, da ke nuna ya amince da zabensa na takarar mataimakin shugaban kasa.

Peter Obi da Datti Baba-Ahmed sun halarci zaman kotu

Dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi da abokin takararsa a zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu, Datti Baba-Ahmed, yanzu suna kotu.

Kotun ta amince da daga karar APM kan hukuncin da ta yanke dangane da shari'ar takara biyu da PDP ta shigar

Bisa bukatar lauyan na APM, Alkalan biyar karkashin jagorancin Mai shari'a Haruna Tsammani sun dage karar zuwa ranar Juma'a don cigaba da shari'ar APM.

Jam'iyyar Labour ta fara gabatar da korafinta, ta gabatar da shaida daya

Jam'iyyar Labour, LP, ta fara gabatar da kararta ta hanyar kirar shaida guda daya.

Tunda farko, kotun ta ware awa uku don sauraron karar na LP da dan takarar shugaban kasarta, Peter Obi.

Amma, da aka tambaye su yawan shaidun da suke da shi a kotun yau, Livy Uzoukwu (SAN) ya ce masu shigar da karar shaida daya kacal suke da shi a yau.

Lauyan APC ya yi kafa hujja da hukuncin kotun koli kan shari'ar PDP

An fara shari'ar ne da Bola Tinubu, ta hannun lauyansa Wole Olanipekun ya kafa hujja da hukuncin da kotun kolin ta yi a baya-bayan nan ranar Juma'a 26 ga watan Mayu, na korar karar zargin cewa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya yi takara sau biyu.

Olanipekun ya yi tambaya ko wancan hukuncin ya soke karar da jam'iyyar APM ta shigar, ita ma na kallubalantar sauya Kabir Masari da Kashim Shettima.

A martaninsa, S.A.T. Abubakar, lauyan APM ya ce bai riga ya samu kwafin hukuncin da kotun kolin ta yanke ba.

Abubakar ya ce jam'iyyar da ya ke wakilta za ta yi kokarin samun hukuncin don fahimtarsa.

Lauyan Tinubu ya bayyana niyarsa na samun kwafi na ainihi na hukuncin domin ya ba wa APM.

A martansinsa, lauyan APM ya bukaci a dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar Juma'a 2 ga watan Yuni domin ba shi damar neman kwafin hukuncin na kotun koli dangane da batun takara biyu na Shettima.

30 ga Watan Mayu: Kotun karar zaben shugaban kasa ta cigaba da zamanta

Barka da zuwa shafin bayanai kai tsaye na Legit.ng Hausa kan zaman da ake yi a kotun sauraron karar zaben shugaban kasa a yau Talata 30 ga watan Mayu.

Abin da ake tsammani yau shine ainihin sauraron korafi na kallubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023.

Kotu ta tsayar da ranar fara sauraron kararraki

A bangare guda, kotun ta tsayar da ranar 30 ga watan Mayu don fara sauraron kararrakin gadan-gadan.

Kotun ta ba wa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, sati uku domin ya gamsar da kotu da hujjoji dangane da sakamakon zaben shugaban kasar.

A rahoton sharen fage da Mai Shari'a Tsammani ya karanto, ya ce satin ukun ya fara daga ranar 30 ga watan Mayu zuwa 23 ga watan Mayu.

Don tabbatar da kammala shari'ar a kan lokaci, ba za a yi wa shaidu tambaya da baka ba, kawai kalamansu a rubuce za a yi amfani da shi. Ga manyan shaidu ko (kwararrun shaidu), za a bawa babban mai gabatar da shaida minti 30 ya musu tambaya, sannan lauya ya yi minti 20 wurin musu tambaya sai karin minti biyar don bita kan tambayoyin.

Sannan kotun ta tsayar da ranar 5 ga watan Agusta ga dukkan lauyoyin Obi su kammala gabatar da kararsu, hakan na nufin sai jiran hukunci.

Bisa jadawalin, ana sa ran kotun za ta rika zama daga Litinin zuwa Asabar a kowanne mako har sai an kammala sauraron kararrakin.

Bisa tanadin doka, kotun na da kwana 180 don sauraron korafe-korafe kuma hakan zai zo karshe a ranar 16 ga watan Satumban 2023.

Kotu ta gwamutse kararrakin APM, Peter Obi da Atiku Abubakar

Tinubu da APC ba su yi nasarar dakatar da kotun gwamutse kararrakin Atiku, Peter Obi da jam'iyyar APM ba.

Kotun a ranar Talata ta gwamutse dukkan kararrakin da aka shigar kan Tinubu.

Idan za a iya tunawa a baya kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasar ta tada batun hade kararrakin wuri guda kuma ta bukaci bangarorin su duba yiwuwar hakan.

Tinubu da APC ba su amince da batun gwamutsa kararrakin ba, amma sauran wadanda suka shigar da karar suka ce ba su da zabi kan lamarin.

Bayan da kotu ta fara zama a yau Talata, alkalan biyar na kotun sun ce za a gwamutse kararrakin kuma a saurare su tare saboda karancin lokaci don a wareware matsalar.

Talata, 23 ga watan Mayu: Kotun karar zaben shugaban kasa ta cigaba da zama

Kotun sauraron kararrakin shugaban kasa ta cigaba da zamanta a yau Talata, 23 ga watan Mayu. Me ake tsammanin zai faru a yau?

Alkalai za su bada rahoto kan sauraron korafi na sharar fage da aka shafe makonni biyu ana yi.

Kotun mai alkalai biyar karkashin Mai Shari'a Haruna Tsammani za ta bayyana matsayarta kan batun gwamutse kararraki uku Atiku/PDP, Peter Obi/Jam'iyyar Labour da APM suka shigar.

Kotun sauraron karar zaben shugaban kasa ta ki amincewa da bukatar haska shari'ar kai tsaye da Atiku da Peter Obi suka bukata

Kotun ta yi watsi da bukatar neman haska zaman shari'ar kai tsaye ta kafar talabijin da intanet.

A hukuncin da alkalan biyar suka yi tarayya, kotun ta ce dokokin Najeriya bai bada damar a rika haska shari'a kai tsaye ba ta talabijin ko intanet.

An yi watsi da bukatar saboda rashin inganci domin yin hakan zai zama tamkar mayar da shari'ar a matsayin dirama.

Karanta karin bayani a nan.

APC ba ta amince a gwamutsa kararraki ukun ba

Jam'iyyar APC ta bakin lauyanta, Charles Edosomwan, ta ki amincewa da batun gwamutse kararraki uku da aka shigar kanta da INEC yana mai cewa hakan ba zai haifar da adalci ba duk da cewa kotu ke da hurumin daukan mataki kan batun.

APM tana da shaida daya

Jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta ce tana da shaida guda daya kuma ta nemi a ba ta kwana biyu domin gabatar da kararta na kallubalantar Tinubu.

Jam'iyyar kuma ta ce a shirye ta ke a gwamutse kararta da sauran ukun.

A bangaren hade kararrakin, INEC ta ce kotu ne ke da hurumin daukan mataki kan hakan.

Hukumar zaben ta ce ba ta da na cewa kan batun gwamutse kararrakin.

Litinin, 22 ga watan Mayu: An cigaba da zaman sauraron shari'a

Litinin, 22 ga watan Mayu: An cigaba da zaman sauraron shari'a

Kotun sauraron kararrakin zabe ta cigaban da zamanta a yau Litinin 22 ga watan Mayu, inda ake sa ran samun hukunci kan bukatar da PDP da Labour ta shigar na neman a haska shari'ar kai tsaye.

Alkalan biyar karkashin jagorancin Mai shari'a Haruna Tsammani za su yanke hukunci kan bukatar da INEC, da Bola Tinubu ba su amince da shi ba.

Hakazalika, za a yanke hukunci kan duba yiwuwar hade kararraki uku da suka rage.

Kararrakin da suka rage su ne na jam'iyyar PDP, Jam'iyyar Labour da Allied Peoples Movement (APM).

Dukkansu suna neman a soke nasarar Tinubu a zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Atiku zai gabatar da shaidu guda 100 a kotu

Lauya da ke wakiltan Atiku/PDP ya sanar da kotu cewa wanda ya ke karewa zai gabatar da shaidu a kalla guda 100 a yayin shari'arsu ta kallubalantar nasarar Tinubu a zaben.

Sun nuna niyyarsu ta kammala gabatar da korafinsu cikin sati uku, duk da cewa suna da damar yin hakan cikin sati bakwai a matsayin masu shigar da kara.

Tinubu zai gabatar da shaidu 39 a karar Atiku da PDP

A cewar Roland Otaru, lauya mai wakiltar Tinubu, suna shirin kawo shaidu 39 da nufin cike gurbinsu a karar cikin kwana tara.

Otaru ya kara da cewa ya kamata a gabatar da duk wani rahoto daga 'kwararren mai bada shaida' awa 48 kafin su bayyana gaban kotu don bada shaidan.

Hakazalika, lauyan na Tinubu ya jadada muhimmancin gabatar da takardu daga dukkan bangarorin gabanin ranakun da za a kira shaidu.

INEC za ta gabatar da shaidu biyu yayin sauraron karar Atiku/PDP

INEC, ta hannun lauyanta, Abubakar Mahmoud, ta ce za ta gabatar da shaidu biyu yayin sauraron karar da Atiku/PDP suka gabatar na kallubalantar sakamakon zaben.

Abin da ake tsammanin zai faru a kotun sauraron karar zaben

Ana tsammanin kotun za ta daidaita yadda za ta saurari korafin jam'iyyar PDP da na Labour, a cewar Channels TV.

Jam'iyyun biyu na kallubalantar nasarar dan takarar APC kuma zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.

Chris Uche, lauyan dan takarar PDP Atiku Abubakar, da jam'iyyarsa, ya ce dukkan bangarorin sun hadu sun cimma matsaya kan adadin shaidu, da lokacin da za a bada don yi wa shaidun tambaya.

Asabar, 20 ga watan Mayu: Kotun sauraron karar zabe ta cigaba da zama

Barka da zuwa zauren rahotanni kai tsaye daga Legit.ng Hausa, yau Asabar, 20 ga watan Mayu.

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Peter Obi tare da wasu manyan yan PDP sun halarci kotun.

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel