Kaduna: Babban Abinda Ya Sa Ban Yi Shagalin Lashe Zaben Gwamna Ba, Uba Sani
- Zababben gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya ce ba halinsa bane shirya bikin murna bayan samun nasarar zabe
- Maimakon haka, Sanatan Kaduna ta tsakiya ya ce Malamai sun gudanar Addu'ar godiya ga Allah bayan azumin watan Ramadan
- Ya sha alwashin cewa zai tafi da kowane ɓangaren Kaduna a gwamnatinsa da zaran ya karbi mulki ranar 29 ga watan Mayu
Kaduna - Zaɓabɓen gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bayyana abinda ya sa bai shirya shagalin murna kan nasarar da ya samu ba a babban zaben 2023.
Sanata Uba Sani ya ce bai shirya taron murna ba bayan ya ci zaɓe saboda ya maida hankali kan nauyin da Al'umma suka ɗora masa a matsayinsa na Sanatan Kaduna ta tsakiya.
A wata hira da sabon gwamna ya yi cikin harshen Hausa a Kaduna, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa ya gudu daga Kaduna bayan sanar da sakamakon zaɓe.
Daily Trust ta rahoto cewa Uba Sani ya yi bayanin cewa ba ɗabi'arsa bace ya shiga irin waɗan nan shagulgulan na zamani da 'yan adawa ke tsammani, ya ce a wurinsa ba daidai bane.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce maimakon haka, Malaman addinin Musulunci da Kiristoci suka gudanar Addu'o'in rokon Allah ya taimaka masa a matsayin mutum lamba ɗaya a jihar Kaduna.
Gwamna mai jiran gado a Kaduna ya ce:
"Yan adawa sun ce ban yi murnar samun nasara da irin shagulgulan nan ba, lallai ba su san wanene Uba Sani ba, ba ɗabi'a ta bace na shirya wannan fitsarar da sunan bikin murna."
Yadda na gode wa Allah bayan lashe zaɓe - Sani
Zababben gwamnan ya ƙara da cewa bayan kammala azumin watan Ramadan, an tara Malamai sun karanta littafin Allah mai tsarki wato Alkur'ani domin gode masa bisa wannan nasara.
"Sun roki Allah, kamar yadda ya bamu nasara, ya taimake mu wajen tafiyar da mulkin Kaduna ta hanyar da ta dace," inji shi.
Uba Sani ya ce Fastoci ma sun zo sun masa Addu"a da jiha baki ɗaya. Ya kuma yi alkawarin tafiya da kowane ɓangaren Kaduna da zaran ya karbi mulki ranar 29 ga watan Mayu, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Wani mamban APC kuma shugaban wata ƙungiyar Mobilization a ƙaramar hukumar Kaduna South da ke cikin birnin Kaduna ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa da ƙyar suka sha a zaben 2023.
A wata hira da wakilinmu, Zaharadden Aliyu, ya ce jam'iyyarsu APC ta sha baƙar wahala kafin samun nasara a Kaduna kuma sun yi farin ciki duk da babu wani taro da aka shirya.
"Banga laifin sabon gwamnan mu ba don bai shirya irin waɗan nan taruka ba, kamar yadda ya faɗa yana da wani nauyin a kansa wato matsayin Sanatan Kaduna ta tsakiya."
"Amma game da zaɓen gwamnan da ya wuce, a zahirin gaskiya da kyar muka iya kawo Kaduna, mun gode wa Allah bisa nasarar da ya bamu, shi kuma Malam Magajin Malam Allah ya dafa masa."
Majalisa ta amince Buhari ya ƙara ciyo bashi
A wani labarin na daban kun ji cewa Majalisar Tarayya Ta Amince Wa Shugaba Buhari Ya Kara Karbo Bashi Bisa Sharadi
Majalisa ta amince Buhari ya ƙara sunkuto bashin dala miliyan $800m, amma Kwamitin kula da ciyo bashi ya ce za'a bar kuɗin har sabuwar gwamnati ta kama aiki.
Asali: Legit.ng