Dalilai 6 Da Za Su Wargaza Hukuncin Kotun Kano Na Soke Takarar Alex Otti, Fitaccen Lauya Ya Magantu

Dalilai 6 Da Za Su Wargaza Hukuncin Kotun Kano Na Soke Takarar Alex Otti, Fitaccen Lauya Ya Magantu

  • Wani sanannen lauya mai suna Festus Ogun ya kalubalanci Mohammed Yunusa akan hukuncin da ya yanke akan Alex Otti
  • A martaninsa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Ogun ya ce wannan hukunci na Yunusa ba inda za ta je a dokar zabe
  • Lauyan ya lissafo dalilai shida da yake ganin cewa wanda ya yanke hukuncin a Kano, Mohammed Yunusa ya yi kuskure

FCT, Abuja - Wani sanannen lauya a Najeriya mai suna Festus Ogun ya ce hukuncin da kotun tarayya da ke Kano a ranar Alhamis 18 ga watan Mayu bai inganta ba.

Idan baku manta ba, kotu ta soke tikitin zababben gwamnan Abia Alex Otti da sauran ‘yan takarar jam’iyyar Labour a jihar Abia da Kano.

Lauya Festus bai yadda da hukuncin kotun ba
Lauya Festus Ogun Bai Yadda da Hukuncin Kotu Akan Rusa Zaben Gwamnan Abia Alex Otti Ba. Hoto: Alex Otti, Festus Ogun
Asali: Facebook

Da yake yanke hukuncin bayan shigar da kara da Ibrahim Haruna Ibrahim ya yi, Mai Shari’a Mohammed Yunusa ya ce takarar wadanda ake magana akansu duka ba a kan ka’ida suke ba, jaridar Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ba Sassauci: Yana Dab Da Sauka Mulki, Gwamna El-Rufai Ya Sha Wani Muhimmin Alwashi

Alex Otti: Ba za ka rusa nasarar wanda aka riga aka sanar cewa ya yi nasara ba.

Da yake maida martani a shafinsa na Twitter, Festun Ogun a ranar Juma’a 19 ga watan Mayu ya kalubalanci wannan hukunci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya fadi dalilansa

Ya ce: wannan hukunci bai inganta ba, ga dalilai.
1. An shigar da karar wata daya bayan kammala zabe kuma an sanar da Alex Otti a matsayin wanda yayi nasara.
2. Mutanen da abin ya shafa ba su hadu a matsayin jam’iyya ba a karar.
3. Waye ne Ibrahim Haruna Ibrahim? A karkashin dokan zabe, dan takara ne kawai zai iya kalubalantar sakamakon zabe.
4. Maganar mambobin jam’iyya matsala ce ta cikin gida wanda kotu ba ta da hurumin shiga.
5. Wannan karar ba abinda zai sauya tun da an riga an gudanar da zabe

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Cigaba da Fitowa Kan Mutanen da Tinubu Zai Ba Mukamai a Gwamnati

6. Wannan karar ta sabawa doka, hukuncin ba za ta jure bincike ba, za a wargaza ta a kotun daukaka kara.

Festus Ogun ya rubuta a shafinsa na Twitter:

Kotu Ta Soke Tikitin Takarar Zababben Gwamnan Abia, Alex Otti a Kano

A wani labarin, babbar kotun tarayya dake Kano ta soke tikitin takarar zababben gwamnan Abia Alex Otti na jam'iyyar Labour.

Har ila yau kotun ta soke takarar wasu da jam'iyyar Labour ta tsayar a jihohin Abia da Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.