Zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu, Zai Dawo Najeriya Ranar Lahadi

Zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu, Zai Dawo Najeriya Ranar Lahadi

  • Shugaban kasa mai jiran gado a Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai dawo Najeriya daga Faransa ranar Lahadi
  • Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas ya shirya dawowa gida yayin da ake saura kwanaki kalilan ya ɗare kan madafun iko
  • Idan baku manta ba kakakin Tinubu ya ce zababben shugaban kasa zai amfani da zamansa a Faransa wajen shirya karɓan mulki

Ana sa ran zababbben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai dawo gida Najeriya daga birnin Faris na ƙasar Faransa ranar Lahadi 21 ga watan Mayu, 2023.

Bola Tinubu, wanda ke dab da hawa kan kujerar shugabancin Najeriya, zai dawo gida daga tafiyar da ya yi ana sauran kwanaki 8 rantsarwa wacce zata gudana ranar 29 ga watan Mayu.

Bola Ahmed Tinubu.
Zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu, Zai Dawo Najeriya Ranar Lahadi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Rahoton Leadership ya ce wata majiya mai kunsaci da shugaba mai jiran gado ta ce Tinubu zai baro Faransa bayan kwashe kwanaki 9 yana tattaunawa da masu zuba hannun jari.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Shugaba Buhari Ya Sanar da Muhimmin Abu 1 da Zai Wa Tinubu da Shettima Kafin Ya Sauka

A cewar majiyar bayan kokarin jawo masu zuba hannun jari, Tinubu ya yi amfani da zamansa a Faransa wajen tsara shirin karban mulki, "Ba tare 'yan kamun ƙafa sun takura masa ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yaushe Tinubu zai diro gida Najeriya?

Majiyar ta ƙara da bayyana cewa ana tsammanin jirgin Asiwaju zai dira a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe, ranar Lahadi a Birninn Tarayya Abuja.

A kalaman Majiyar ta ce:

"Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, shugaban ƙasa mai jiran gado zai taso daga birnin Faris zuwa Abuja ranar Lahadi."

Idan baku manta ba, zababben shugaban ƙasa ya sake sa ƙafa ya fice daga Najeriya makonni biyu kacal bayan ya dawo daga Faransa inda ya kwashe kusan wata guda yana hutu.

A sanarwan da mai magana da yawun Tinubu, Tunde Rahman, ya fitar, ya ce wannan tafiyar zata taimaka wa zababben shugaban ya tsara shirin karban mulki ba tare da an damesa ba.

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Cigaba da Fitowa Kan Mutanen da Tinubu Zai Ba Mukamai a Gwamnati

Ganduje ya maida martani ga zababben gwamnan Kano

A wani rahoton na daban kuma Gwamna Ganduje ya tona yadda Kwankwaso ya kawo tsarin sayar da gidajen gwamnatin Kano tun a mulkinsa.

Dakta Ganduje ya bayyana haka ne a wani sautin murya, yayin martani ga shirin zababben gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262