Majalisa Ta 10: Gwamnonin Arewa Na APC Ba Zasu Saba Wa Tinubu Ba, Sule

Majalisa Ta 10: Gwamnonin Arewa Na APC Ba Zasu Saba Wa Tinubu Ba, Sule

  • Gwamnonin arewa a inuwar APC ba zasu yi jayayya da Bola Tinubu ba kan shugabancin majalisar tarayya ta 10
  • Gwamna Abdullahi Sule ne ya faɗi haka yayin da ya karbi bakuncin ɗan takarar kakaki da mataimakin kakakin majalisa wakilai a Abuja
  • Ya ce duba da yadda gwamnonin suka marawa Tinubu baya tun farko, ba zasu dawo su yaƙe shi a majalisa ba

Abuja - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya tabbatar da matsayar gwamnonin arewa na jam'iyyar APC game da shugabancin majalisar tarayya ta 10.

Gwamna Sule ya ce shi da takwarorinsa gwamnonin APC na arewacin Najeriya ba zasu saɓawa waɗanda zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu, yake son su jagoranci majalisa.

Gwamna Sule da yan takara.
Majalisa Ta 10: Gwamnonin Arewa Na APC Ba Zasu Saba Wa Tinubu Ba, Sule Hoto: Gov Abdullahi Sule
Asali: Facebook

The Nation ta rahoto cewa Sule ya bayyana haka ne lokacin da 'yan takarar da APC ta tsayar a matsayin kakaki da matainakin kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen da Benjamin Kalu suka kai masa ziyara a Abuja.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gbajabiamila Ya Ce Ya Yi Nadamar Goyon Bayan Tambuwal Da Ya Yi Ya Zama Kakakin Majalisa

Sule ya ce baki ɗaya gwamnonin arewa masu biyayya ne ga uwar jam'iyya kuma ba abinda suka tasa a gaba illa yadda gwamnatin Tinubu mai zuwa zata ci nasara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan ya kara da cewa Tinubu ya nuna 'yan takarar da yake ƙaunar su shugabanci majalisar tarayya, kuma ina ganin babu wanda zai saɓa masa kan haka.

Ana neman kawo matsala ga jam'iyya

A cewarsa, yaƙar zaɓin shugaban kasa mai jiran gado da APC tamkar kirkiro matsala ne ga gwamnati mai kamawa.

Ya kafa hujja da cewa gwamnonin arewa ne suka kai gwauro suka kai mari kan tilas mulkin ƙasa ya koma kudancin Najeriya bayan karewar wa'adin Buhari.

"Don haka idan mutane su ka ji muna jayayya da zababben shugaban kasa dariya zasu mana, ba zamu saɓa masa ba. Ba zamu yaƙi zabin Tinubu da jam'iyyarmu ba."

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Yi Fatali da Shirin Gwamnonin Arewa 5, Ya Faɗi Wanda Yake Goyon Baya a Majalisa Ta 10

Zamu zauna da Tinubu - Sule

Gwamnan ya tabbatar da cewa da zaran shugaban kasa mai jiran gado ya dawo Najeriya, "Zamu zauna da shi mu tambaye shi me aka ware wa arewa ta tsakiya."

"Ni gwamna ne, idan na nuna alamun wanda nake so ya zama kakakin majalisar dokokin jihata, babu mai jayayya da ni."

Banda gida a kashen ketare - Buhari

A wani labarin kuma Shugaba Mai Barin Gado, Muhammadu Buhari, Ya ce Bai Mallaki Ko Gida ɗaya ba a ƙasashen ketare.

Yayin da wa'adinsa ke dab da cika ranar 29 ga watan Mayu, 2023, Buhari ya ce ko inci ɗaya bai mallaka ba a wata ƙasa daban da Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262