Doguwa, ‘Yan APC 2 Sun Hakura da Kujerar Majalisa, Sun Ayyana ‘Dan Takararsu
- Takarar Majalisa ta canza domin Alhassan Ado Doguwa ya koma goyon bayan Hon. Tajuddeen Abbas
- ‘Dan majalisar na Tudun Wada da Doguwa ya halarci taro inda aka ga Abbas da Hon. Benjamin Kalu
- Hon. Doguwa ya tabbatar da cewa ya fasa neman takara a majalisa tun da APC ta raba masu gardama
Abuja - Alhassan Ado Doguwa wanda shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya, ya hakura da kujerar da yake burin samu a majalisa.
Rahoton da aka samu daga The Cable, ya tabbatar da cewa a halin yanzu Honarabul Alhassan Ado Doguwa bai cikin masu takarar shugabancin majalisa.
Alhassan Ado Doguwa ya sanar da hakan ne a ranar Laraba da daddare lokacin da ya gana da wasu zababbun ‘yan majalisar tarayya a wani otel a Abuja.
Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da ‘yan takaran da APC ta tsaida, Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu sun halarci zaman da aka yi jiya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ware kujeru ya cire Maki da Olawuyi
Rahoton ya ce Hon. Abubakar Maki da Hon. Olatunji Olawuyi duk sun hakura da takararsa da suka yi niyya a zaben shugabanni majalisa ta goma.
Doguwa ya ce Hon. Abbas mai wakiltar mazabar Zaria ya cancancanta ya jagoranci ragamar mutane 359 da za a rantsar a majalisar wakilan Najeriya.
Hakan ya na zuwa ne bayan an yi tunanin shugaban masu rinjayen ya na cikin masu yakar Abbas, ya na goyon bayan 'yan kungiyar G7 da ke majalisa.
An ragewa 'Yan G7 karfi
‘Dan majalisar na Tudun Wada da Doguwa yake cewa ya hakura da takararsa ne a ranar da jam’iyyar APC ta ayyana Tajuddeen Abbas da Ben Kalu.
Kamar yadda PM News ta fitar da labari a daren yau, Doguwa wanda ya dade a majalisa ya nuna zai goyi bayan Tajudeen Abbas ya gaji Gbajabiamila.
“Ka da ayi tunanin tsautsayi ya kawo ni nan. Masu tunanin mafarki su ke yi, ba mafarki ba ne wannan. Wannan shi ne zahiri.”
- Alhassan Ado Doguwa
Wannan lamari zai taimakawa jam’iyyar APC da ‘yan takaranta a zaben da za ayi a Yuni.
Abbas/Kalu sun samu karbuwa
A baya an samu rahoto cewa takarar Hon. Tajuddeen Abbas da Hon. Benjamin Kalu ta na cigaba da samun goyon baya a Majalisa a kan gungun 'Yan G7.
Wasu Gwamnonin jihohi da kuma ‘yan PDP, LP, SDP, NNPP da sauran jam’iyyun adawa za su marawa Tajuddeen Abbas baya ya zama shugaban majalisa.
Asali: Legit.ng