Da Dumi-Dumi: Rigima Ta Barke Tsakanin Tsagin Jam'iyyar Labour Party a Kotun Zabe
- An samu hatsaniya a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, a tsakanin tsagin jam'iyyar Labour Party
- Rigimar ta fara ne lokacin da shugaban tsagin jam'iyyar, Lamidi Apapa, ya isa kotun domin halartar zaman kotun
- Lamidi da wani jigon jam'iyyar na ɗayan tsagin sun yi musayar kalamai a tsakanin su kan wajen zama
Abuja - An samu hargitsi a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a ranar Laraba, lokacin da rigima ta ɓarke tsakanin tsagin jam'iyyar Labour Party.
Rigimar ta fara ne lokacin da Lamidi Apapa, shugaban tsagin jam'iyyar, ya shigo cikin harabar kotun tare da wasu magoya bayansa, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
Apapa wanda su ke ta taƙaddama da dakataccen shugaban jam'iyyar na ƙasa, Julius Abure, ya isa kotun ne domin sauraron ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Peter Obi, ya shigar inda ya ke ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu, a zaɓen shugaban ƙasa.
Majalisa Ta 10: Takarar Akpabio Da Barau Ta Samu Tagomashi, Wasu Jiga-Jigan Jam'iyyar APC Sun Mara Mu Su Baya
Duk da cewa Abure bai halarci zaman kotun ba, wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar da suka haɗa da Akin Osuntokun, babban darektan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Obi-Datti, suna wajen.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda lamarin ya auku
Rigimar dai ta fara ne lokacin da jami'an kotun suka buɗe harabar kotun ga lauyoyi da waɗanda ƙarar ta shafa domin zaman kotun na ranar.
Mr Osuntokun da wasu jiga-jigan jam'iyyar sun zauna a wurin zaman su cikin kotun, lokacin da Apapa da wasu ƴan tawagarsa suka buƙace su da su tashi daga wajen zaman na su, cewar rahoton Premium Times.
Apapa ya bayyana cewa shine halastaccen shugaban jam'iyyar Labour Party, wanda ya kamata ya zauna a wajen.
Sai dai, Osuntokun ya ƙi bayar da wajen zamansa, inda ya haƙiƙance cewa Apapa baya da hurumin zama a wajen.
Sai da sakataren kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, Josephine Ekperobe, ta sanya baki sannan hankula suka kwanta a tsakanin Apapa da Osuntokun.
An Bayyana Peter Obi a Matsayin Wanda Ya Lashe Zabe a Jihar Rivers Ba Tinubu Ba
A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa an bayyana Peter Obi a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa, a jihar Rivers.
Peter Obi, ɗan takarar shugaan ƙasa na jam'iyyar Labour Party, ba shi bane ya lashe zaɓen a jihar Rivers, a sakamakon da hukumar INEC ta fitar.
Asali: Legit.ng