Tsaffin 'Yan Majalisar APC Sun Marawa Takarar Akpabio Da Barau Baya
- Tsaffin ƴan majalisa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), sun bayyana cewa zaɓin Akpabio da mataimakinsa ya cancanta
- Shugaban tsaffin ƴan majalisar kuma tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai Hon. Babangida Nguroje, ya ce zaɓin da aka yi mu su abin a yaba ne
- Ya kuma yi nuni da cewa ƴan majalisar sun cika dukkanin wasu sharuɗɗa da ake buƙata domin shugabantar majalisar dattawa ta 10
Abuja - Takarar neman shugabancin majalisar dattawa ta 10, da sanata Godswill Akpabio ke yi, ta samu tagomashi bayan ƙungiyar tsaffin ƴan majalisar jam'iyyar APC, sun mara masa baya.
A cewar wata sanarwa da Legit.ng ta ci karo da ita a ranar Talata, 16 ga watan Mayu, tsaffin ƴan majalisar sun bayyana cewa sun yi na'am da hukuncin jam'iyyar na zaɓar sanata Akpabio da Barau Jibrin, a matsayin shugabannin majalisar dattawa ta 10 mai zuwa.
An samu cimma wannan matsayar ne bayan, tsaffin ƴan majalisar sun gudanar da wani taro a birnin tarayya Abuja, domin kawo ƙarshen tirka-tirkar da ake ta sha kan shugabancin majalisa ta 10.
Da ya ke magana kan lamarin a birnin tarayya Abuja, shugaban tsaffin ƴan majalisar na ƙasa kuma tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Hon. Babangida Nguroje, ya ce zaɓin jam'iyyar abin a yaba ne.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Zaɓin Akpabio da Barau ya cancanta - Tsaffin ƴan majalisa
Ya bayyana cewa dukkanin ƴan takarar sun cika sharuɗɗan da ake buƙata, na zama tsohon sanata, sanata wanda ya taɓa riƙe muƙami ko zaɓaɓɓen sanata idan babu wani sanatocin da suka taɓa riƙe muƙami
Nguroje ya bayyana cewa:
"Abin lura ne cewa mai girma sanata (Dr.) Godswill Obot Akpabio (CON) da sanata Barau Jubril, suna da dukkanin wasu halaye da cancantar zama shugabannin majalisar dattawa ta 10 ta tarayyar Najeriya."
Nguroje ya kuma yi kira ga fusatattun sanatocin da ke adawa da matsayar jam'iyyar APC, da su zo su marawa Akpabio da Barau baya, domin an zaɓo su bisa cancanta, gaskiya da adalci.
Yan Majalisar Tsagin Adawa Sun Hakura da Neman Kakakin Majalisa Ta 10
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa ƴan majalisa tsagin adawa sun janye daga takarar kujerar kakakin majalisa ta 10.
Ƴan majalisar waɗanda suka fito daga jam'iyyun adawa daban-daban, sun cimma wannan matsayar ne saboda babu wani daga cikinsu da ya nuna yana buƙatar neman kujerar
Asali: Legit.ng