Mailantarki Bai Karbi Ko Sisin Kwabo Daga Wurin Inuwa ba, Dan Majalisa
- Mamban majalisar dokokin jihar Gombe, Rambi Ayala, ya karyata jita-jitar da ake yaɗawa kan ɗan takarar gwamna a inuwa NNPP
- Ayala ya ce ko da wasa Khamisu Mailantarki bai karbi ko kwandala daga hannun gwamna Inuwa Yahaya don janye masa ba
- Ya ce farfaganda da hukuncin Kotun ƙarya da aka yaɗa ne suka haddasa rashin nasarar NNPP a zaben 2023
Gombe - Shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar Gombe kuma jigon jam'iyyar NNPP, Honorabul Rambi Ayala, ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa kan Khamisu Mailantarki.
Ɗan majalisa ya ƙaryata jita-jitar cewa ɗan takarar gwamna a inuwar NNPP, Mailantarki, ya karɓi biliyan N2bn cin hanci daga hannun gwamna Inuwa Yahaya na APC.
Mista Ayala ya yi fatali da wannan jita-jita yayin zantawa da 'yan jarida jim kaɗan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki, wanda NNPP ta kira domin nazari kan abinda ta tabuka a zaben da ya wuce.
Ɗan majalisar ya tona asirin waɗanda suka ɗauki nauyin yaɗa karya ka Mailantarki
A rahoton Leadership, Ayala ya ce labarin ƙanzon kurege ne wanda jam'iyyar APC ta kirkira da nufin cin fuska da ɓata sunan ɗan takarar NNPP saboda sun ga mutane na ƙaunarsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ƙara da cewa masu adawa da NNPP sun fara zullumi ganin yadda Mailantarki ya baiwa mutane kyaututtuka da tallafi a lokacin kakar zaɓe, shiyasa suka bullo da zargin ai kuɗi ya karba daga gwamna.
A cewarsa saboda yan adawa sun sha jinin jikinsu da ayyukan Alherin Mailantarki, sun rasa me zasu yi don ɓata masa suna, shi ne suka kirkiro jita-jitar gwamna ne ya ba shi biliyan N2bn domin ya janye masa.
Meyasa NNPP ta sha kashi a zaben gwamnan Gombe?
Ayala ya ce Farfaganda da umarnin kotu na karya da aka yaɗa wanda ya nuna cewa Kotu ta soke tikitin ɗan takara NNPP ne ya jawo wa jam'iyyar rashin nasara.
Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini
Ya ce:
"PDP na cikin fargaba, gwaamnati mai ci da jam'iyyar APC suna cikin zullumi, saboda haka suke kawo Farfaganda da rahoton karya don ta haka ne kaɗai kayansu zasu yi kasuwa."
A wani labarin kuma kun ji cewa Gwamnoni 5 a Arewa Sun ki Amincewa da Yadda Aka yi Kason Kujerun Majalisa a Jam'iyyar APC
Gwamnonin shiyyar Arewa ta Tsakiya a Najeriya sun bukaci jam'iyyar APC ta sake nazari kan yadda ta raba manyan kujerun majalisar tarayya ta 10.
Asali: Legit.ng