APC: Gwamnoni 5 a Arewa Sun ki Amincewa da Yadda Aka yi Kason Kujerun Majalisa
- Gwamnonin jihohin Arewa maso tsakiya sun fitar da matsayarsu a kan shugabancin majalisa
- Sani Bello da sauran abokan aikinsa sun nemi APC ta sake duba yadda tayi kason kujerun majalisa
- Wadannan Gwamnoni sun goyi bayan ‘yan majalisun yankinsu, su na ganin ba ayi masu adalci ba
Abuja - Gwamnonin jihohin Arewa maso tsakiya sun nuna rashin goyon bayansu ga tsarin kason mukaman majalisar tarayya da jam’iyyar APC tayi.
This Day ta ce Gwamnonin nan sun cin ma wannan matsaya a karshen doguwar tattaunawar da suka yi tsakaninsu ranar Litinin a birnin Abuja.
Kafin nan Gwamna Yahaya Bello da Abdulrahman Abdulrazaq sun yi zama a baya, sun kuma nuna su na goyon bayan matsayar Sanatocin yankinsu.
Kan Arewa ta tsakiya ya hadu
A matsayinsa na shugaban kungiyar gwamnonin yankin, Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya sa hannu a kan matsayar da dukkansu ke kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran wadanda suka sa hannu sun kunshi: Simon Lalong (Filato); Abdulrahaman Abdulrazaq (Kwara); Abdullahi Sule (Nassarawa); Yahaya Bello (Kogi).
Haka zalika zababben Gwamnan Benuwai, Fr Hyacinth Alia ya na tare da gwamnonin. Nan gaba za su sake zama domin a warware matsalar.
Vanguard ta ce Sanata Mohammed Sani Musa, Hon. Ahmed Idris Wase, da Yusuf Gagdi sun rattaba hannunsu a karshen dogon zaman da aka yi a jiya.
"Matakin da aka dauka shi ne za a goyi bayan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, sannan aka bukaci APC NWC ta sake duba kason kujerun majalisa.
Zaman ya tattauna a kan yadda aka ware kujerun mataimakin shugaban majalisar dattawa da shugaban majalisar wakilan tarayya zuwa wani yanki.
Taron ya amince ayi amfani da lalama da tattaunawa wajen shawo kan sabanin shugabancin majalisa, an amince za a tuntubi masu ruwa da tsaki.
Gwamnnonin sun amince da matsayar ‘yan takara, sun bukaci zababbun ‘yan majalisa su cigaba da ba zababben shugaban kasa goyon bayan yin nasara.
- Gwamnonin Arewa ta tsakiya
Alkwarin Omo Agege
An samu rahoto Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege ya yi nasara an kai wata jami’ar lafiya ta tarayya zuwa jiharsa ta Delta.
Ovie Omo-Agege ya yi magana ta bakin Sunny Areh, ya ce mutanen Ndokwa za su amfana. Sanatan zai bar kujerar da yake kai a karshen majalisa mai-ci.
Asali: Legit.ng