Ku Cika Alkawuran Da Kuka Dauka Ko A Yi Waje Da Ku, Buhari Ya Shawarci Gwamnoni
- Shugaba Muhammadu Buhari ya shawarci gwamnoni da su yi aiki wa jama’a ko kuma su fadi zabe mai zuwa
- Shugaban ya yi wannan kiran ne a bikin kaddamar da Kungiyar Gwamnoni ta Najeriya a birni tarayya Abuja
- Buhari ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari wurin taron
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya shawarci gwamnoni zababbu da wadanda suka samu nasarar komawa karo na biyu da su shirya faduwa in har basu tsinana wa jama’a komai ba.
Buhari ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin 15 ga watan Mayu a wurin kaddamar da Kungiyar Gwamnoni ta Najeria (NGF).
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa bikin an gudanar da shi ne a babban dakin taro na Banquet dake fadar shugaban kasa a Abuja saboda gwamnonin su samu kwarewa don gudanar da mulkinsu na dimukradiya cikin nasara.
Shugaba Buhari wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan gwamnati na tarayya Farfesa Ibrahim Gambari ya ce dole ‘yan Najeriya su zama masu hakuri da kuma sanin hanyoyin da zasu bi wurin kwato hakkokinsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Buhari ya ce nan da zuwa 29 ga watan Mayu za a rantsar dasu zuwa shekaru 4, daga wannan rana zasu kasance sun dauki nauyin jama’a a karkashinsu.
“Abun burgewa anan shine yadda muka ga zaben da ta gabata wadda kullum kara ci gaba take, mutane suna fahimtar ‘yancinsu, duk wani gwamnan da ya gagara cika alkawuran da ya dauka tabbas zai gani a kwaryar tuwonsa, kayi aiki ko ayi waje dakai,” in ji shi.
Buhari ya bai wa gwamnoni shawarwari kan kawo karshe matsaloli
“Ina umartanku daku samo hanyoyin da zasu kawo karshen matsalolin da dimukradiya ke ciki a kasarmu, hakan shi zai kawo mana ci gaba a kasa ta kowane bangare," in ji Buhari.
Ya kara da cewa:
“Ina shawartarku da kuyi amfani da wannan dama wurin hada kan 'yan kasa ba tare da bambancin jam’iyya ba, kasarmu na bukatar zaman lafiya da ci gaba da kuma tsaro, kasa da za a samu ingantaccen ilimi da lafiya da sauran ababan more rayuwa.”
Buhari Ya Shilla Ingila Don Halartar Nadin Sarautar Sarki Charles
A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai tafi Landan domin halartar taron nadin sarautar Sarki Charles a Burtaniya.
Buhari zai samu rakiyar kusoshin gwamnatinsa da suka hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da ministan harkokin waje, Geoffrey Onyema da ministan yada labarai, Lai Mohammed.
Asali: Legit.ng