Bode George: Jigon PDP Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Zai Taba Ziyartar Tinubu Ba Duk Da An Roke Shi

Bode George: Jigon PDP Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Zai Taba Ziyartar Tinubu Ba Duk Da An Roke Shi

  • Babban jigo a jam’iyyar PDP, Cif Bode George, ya ce ba zai taba ziyartar zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu ba
  • Ya bayyana cewa ba ya jin haushin tsohon gwamnan na Legas, amma ba zai yiwu ya kai masa ziyara a matsayinsa na ɗan adawa ba
  • Jigon na PDP wanda ya bayyana cewa yaran Tinubu sun yi zama da shi, ya ce sun zo ne kawai don ba shi haƙuri kan abubuwan da suka faru a baya

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa Cif Bode George ya bayyana cewa yaran zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu sun zo wurinsa.

George ya bayyana cewa ya amince ayi zaman ne saboda tsohon mai shari’a Isola Olorunmibe mai shekaru 94 ne ya jagoranci mutanen.

Jigon na PDP ya ƙara da cewa ba zai iya ƙin amsa buƙata daga dattijo kamar Olorunmibe ba.

Kara karanta wannan

Ta Fasu An Ji: An Fallasa Abinda Tinubu da Gwamna Wike Su Ke Kulla Wa Atiku Abubakar a Kotu

Bode George/Bola Tinubu/Zababben shugaban kasa
Cif Bode George ya yi barazanar zai yi hijira daga Najeriya zuwa Ghana idan aka rantsar da Tinubu shugaban kasa.. Hoto: Channels TV
Source: UGC

Bode George ya sha alwashin barin ƙasa in Tinubu ya yi nasara

Gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Bode George ya sha alwashin barin Najeriya zuwa ƙasar Ghana idan Tinubu ya zama shugaban ƙasar Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, George ya bayyana cewa:

“Baba Olorunmibe, dattijo mai shekaru 94 ne ya jagorance su. A kasar Yarbawa, dattijo kamar wannan ba zai ce ya na so ya zo gidana ba, ni kuma in ce a’a. Ba bu hakan a al'adata. Akwai kuma wasu dattawan PDP a wurin.”

Sun nemi George ya marawa Tinubu baya

A yayin da ya ke magana dangane da maƙasudin taron, George ya bayyana cewa mutanen Tinubu sun zo ne domin ba shi haƙuri kan wasu abubuwa da suka wakana a baya, tare da roƙonsa ya marawa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar baya.

Kara karanta wannan

"Mahmud Yakubu Tsohon Yaro Na Ne," Pater Obi Ya Fallasa Maganar da Ya Faɗa Wa Shugaban INEC Gabanin Zaben 2023

Ya bayyana cewa wakilan na Tinubu sun buƙaci ya ziyarci zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, tayin da nan take ya ƙi amincewa da shi.

Ya ƙara da cewar sun zo ne kan neman afuwa kan abubuwan da suka faru a baya, inda ya faɗa musu cewa komai ya wuce a wurinsa, kuma ba shi da wata matsala da uban gidan nasu.

Sannan ya ce sun buƙaci ya kai ziyarar ban girma ga uban gidansu, tayin da ya ƙi amincewa da shi, kasantuwarsa babban jigo daga yankin kudu maso yamma a jam'iyyar PDP.

Sannan ya ƙara da cewa babu yadda za a yi ya amince da tayin a yayin da jam’iyyarsa ta PDP ke ci gaba da yaƙin neman ƙwato haƙƙinta hannun zaɓaɓɓen shugaban ƙasan a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.

Jaridar This Day ta ruwaito cewa wasu manyan APC na ƙoƙarin ganin Bode George ya daina yawan sukar da yakewa Tinubu a kafafen watsa labarai.

APC na tattaunawa da abokan gabar Tinubu

A rahoton da Legit.ng ta wallafa a baya, kun ji cewa jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta fara tattaunawar zaman lafiya da wasu manyan abokan hamayyar zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Wakilan APC sun zauna da Bode George wanda jigo ne a jam’iyyar adawa ta PDP domin sasantawa da shi a kan ya marawa Tinubu baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng