Sanatan APC Ya Sha Gaban Yari a Takarar Majalisa, Ya Fadi Sanatocin da ke Tare da Shi

Sanatan APC Ya Sha Gaban Yari a Takarar Majalisa, Ya Fadi Sanatocin da ke Tare da Shi

  • Godswill Akpabio yana ganin tuni ya kama hanyar zama shugaban majalisar dattawa a Najeriya
  • Tsohon Gwamnan na Akwa Ibom ya ce Sanatoci kusan 70 ke goyon bayan shi, kuma za su iya kai 86
  • Sanata Akpabio ya shaida haka ne a lokacin da ya gana da Gwamnan Legas, Babajide Sanwo Olu

Lagos - Tsohon Gwamna a jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio ya ce yana da goyon bayan da yake bukata domin ya jagoranci majalisar dattawa.

A ranar Lahadi, Punch ta rahoto Sanara Godswill Akpabio yana mai cewa Sanatoci 86 yake sa ran za su zabe shi ya zama shugaban majalisar dattawa.

Akpabio ya na tare da jam’iyyar APC a zaben majalisa da za ayi a watan Yuni, a karshen mako ne ya ziyarci Gwamnan Legas, Babajdie Sanwo-Olu.

Kara karanta wannan

Tinubu Ba Zai Manta Ganduje, El-Rufai, Sauran Gwamnonin Arewa a Rabon Mukamai ba

Sanatan APC
Gwamnan Legas da 'Yan Majalisar Dattawa Hoto: von.gov.ng
Asali: UGC

Sanatan ya ce a yanzu akwai Sanatoci 69 da suke tare da shi, kuma yana kara samun goyon baya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

'Yan Akpabio/Barau sun kai 69

"A yau adadinmu ya kai kusan 69 kuma yana karuwa ne. Mun yi imani zuwa lokacin da aka shiga Yuni, mu na sa ran adadinmu ya kai 85 zuwa 86.
Abin da na sani kurum shi ne za mu yi nasara.
Ina so in tabbatar maka da cewa mutanen da ke zaune a nan su ne suka yi watsi da masu rabon Daloli da fan Sterling, suka ki karbar Nairori.
Majalisar dattawa kunshe ta ke da mata da maza masu daraja. Ba za mu bari a saida Najeriya ba.
Idan aka koma saida mukami da kudi, ina tunani da irinsu Marigayi Yar’Adua ba su yi mulkin Najeriya ba, ko Obasanjo ba zai yi mulki ba.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisar Dattawa: Yari, Kalu da Musa Sun Kai Kokensu Wurin Adamu

- Godswill Akpabio

"A ba Tinubu hadin-kai"

The Guardian ta rahoto tsohon Ministan na harkokin Neja Delta yana tir da yadda ake siyasar kudi, sannan Sanwo-Olu ya nuna za su mara masa baya.

Gwamnan jihar Legas ya ba Sanatan da mutanensa kwarin gwiwar lashe zabe, yana mai yin kira ga Sanata Akpabio su ba Bola Tinubu hadin-kai a majalisa.

Alakar 'yan takaran majalisa da EFCC

A wani rahoto an ji yadda Sanata Uzor Kalu ya ke so ya zama shugaban majalisa, amma har gidan yari ya shiga kan satar dukiyar al’ummar jihar Abia.

An yi lokacin da EFCC ta karbe kudi daga asusun Abdulaziz Yari, haka zalika shi ma Godswill Akpabio ma ba bakon hukumar yaki da rashin gaskiyar ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng