Kwana 17 Gabanin Miƙa Mulki, Gwamnan PDP Ya Kaddamar da Aikin da Ba'a Gama Ba
- Kwanaki 17 kacal gabanin mulkinsa ya ƙare, gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya yi abinda ba'a taɓa tunani ba
- Gwamna Ishaku ya kaddamar da rukunin gidaje 500 da ba'a kammala ba a jihar Taraba ranar Alhamis, 11 ga watan Mayu, 2023
- A halin yanzu aikin gina rukunin gidajen wanda gwamnatinsa ta fara a 2017, ya raɗa masa suna Darius Dickson Ishaku (DDI)
Taraba - Gwamnan jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, Darius Ishaku, ya kaddamar da aikin gina rukunin gidajen da ba'a kammala ba ranar Alhamis, 11 ga watan Mayu, 2023.
Premium Times ta rahoto cewa rukunin gidajen wanda aka raɗa wa, "Darius Dickson (DDI) Ishaku Garden Estate," na nan a kan hanyar filin jirgin sama a Jalingo, babban birnin Taraba.
Wane kamfani gwamnati ta baiwa kwangilar gina gidajen?
Bayanai sun nuna cewa gwamnatin Darius Ishaku ta jihar Taraba ta fara aikin gina rukunin gidajen wanda ya ƙunshi gidaje 500 tun a shekarar 2017.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma har zuwa watan Mayu, 2023 ba'a gama gina gidajen ba kuma aikin na haɗaka ne tsakanin gwamnati da masu zaman kansu (PPP).
Bugu da ƙari, rahoton ya ƙara da cewa kamfanin 'Wesany International Concept Ltd' ne ke jagorantar aikin gina gidajen.
Duk da gwamna ya kaddamar da rukunin gidajen ana tsaka da aiki, jaridar ta tattaro cewa kusan dukkan gidajen an kusa kammala su.
Gwamnan ya fitar da N2bn domin sayen motoci
Wannan na zuwa ne awanni bayan gwamna Darius Ishaku ya amince da ware naira biliyan N2bn domin siyo wa kansa da mataimakinsa motocin hawa na Alfarma.
An ce gwamnan ya amince da ware kuɗin a wurin taron majalisar zartaswa ta jihar (SEC) wanda ya jagoranta.
Wata majiya ta bayyana cewa gwamnan ya ɗauki wannan mataki ne saboda shi da mataimakinsa suna amfani da Motoci tun na zangon farko, ba'a sauya masu ba.
Dalilin Da Yasa Gwamnonin Arewa Suka Marawa Tinubu Baya a Zaben 2023, Masari
A wani labarin kuma Gwamna Masari na jihar Katsina Ya Bayyana Ainihin Dalilin da Yasa Suka Tsaya Kai da Fata a Bayan Tinubu.
Gwamnan, wanda ya fara yawon kai ziyarar bankwana, ya ce gwamnonin arewa sun zabi goyon bayan Tinubu ne domin cika alƙawarin tsarin karba-karba.
Haka zalika, Masari ya ce Allah ne ya ceci jam'iyyar APC amma da ace kaye ta sha a zabe da yanzu ba wannan zancen ake ba.
Asali: Legit.ng