Atiku Ya Karfafawa Yan PDP Gwiwa, Ya Ce Har Yanzu Bai Cire Ran Zai Zama Shugaban Kasa Ba

Atiku Ya Karfafawa Yan PDP Gwiwa, Ya Ce Har Yanzu Bai Cire Ran Zai Zama Shugaban Kasa Ba

  • Tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar ya jaddada cewa har yanzu bai yadda ya fadi a zaben ba
  • Atikun ya fadi hakan ne a liyafar da Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar PDP ta shirya ga sabbin gwamnoni
  • Ya shawarshi ‘yan jam’iyyar da su tsaya tsayin daka wurin kawo karshen matsalolin jam’iyyar

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya kara jaddada cewa har yanzu shi kam bai yadda ya fadi zaben da aka gudanar na shugaban kasa ba.

Atiku ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya halarci liyafar da Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP ta gayyace shi don tarban sabbin zababbun gwamnonin jam’iyyar da taya murna ga gwamnonin da suka samu komawa karo na biyu a Abuja a ranar Alhamis 11 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Daga Buhari Zuwa Dogara: Cikakken Jerin Sunayen Shugabannin Majalisar Wakilai Tun 1999 Zuwa Yanzu

Atiku
Atiku Abubakar, Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Dan takarar shugaban kasan ya ce dole su tsaya tsayin daka su kuma hada karfi da karfe don ganin sun kwato wannan mulki da aka wafce a hannunsu ba bisa ka’ida ba, cewar jaridar Tribune.

Ya shawarci ‘yan jam’iyyar da su nutsu su duba yadda jam’iyyar ta samu koma baya, bayan ta kasance jam’iyyar da tafi dadewa da kuma karfi tun shekarar 1999, da kuma halin da yanzu take ciki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atiku ya ce:

“Nan gaba irin wannan biki ya kamata ku sanar mana da wuri saboda mu samu lokacin da zamu tattauna matsalolin jam’iyyarmu da yadda za a shawo kansu.
“Zan yi amfani da wannan dama in taya ku murnan samun nasara, da kuma wadanda suka samu dawowa karo na biyu a ofisoshi daban-daban.”
“Muna da matsaloli daban-daban a wannan jam’iyyar, a baya munfi kowace jam’iyya karfi tun shekarar 1999 amma tun a lokacin muke koma wa baya, lokaci ya yi da ya kamata mu binciki matsalolinmu don mu dawo da martabarmu ta baya.

Kara karanta wannan

An Shiga Jimami Da Zubar Hawaye Yayin Da Tsageru Suka Kashe Aminin Tinubu a Imo

“Mun sani PDP ba ta fadi zaben da aka yi ba, mu tsaya mu natsu mu kwato mulkin da aka sace daga gare mu.”

A jawabinsa, jaridar Punch ta ruwaito tsohon mataimakin Najeriya, Namadi Sambo ya na kira ga ‘yan jam’iyyar da su zauna lafiya, inda ya koka kan yadda rikicin jam’iyya ya yi kamari a matakin jihohi.

Atiku, Obaseki da ManyanJiga-jigan PDP Sun Halarci Babban Taro a Abuja

A wani labarin, Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya halarci babban taron jam'iyyarsu ta PDP tare da jiga-jigan jam'iyyar.

Rahoton ta tabbatar cewa gwamnonin da yawa sun dira wurin taron da wuri wadanda suka haɗa da gwamnan Edo, Godwin Obaseki, takwaransa na Taraba, Darius Ishaku, da Ahmadu Fintiri na Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.