Ziyarar Tinubu Zuwa Rivers: An Zargi Wike Da Tinubu Da Shirya Wata Maƙarƙashiya Kan Atiku
- Ƙungiyar CRPA ta ce ziyarar da Tinubu ya kai ma Wike a Rivers da sunan buɗe ayyuka duk baba-rodo ce, ya je ya bashi wani aiki ne
- Ƙungiyar na zargin Wike da amsar kwangilar tarwatsa duk wasu hujjoji da ka iya taimakawa Atiku Abubakar a wajen shari'ar zaɓe da yanzu haka su ke yi da Bola Tinubu
- Ta kuma zargi cewa, matar Wike, mai shari'a Eberechi Suzzete Wike za ta taka wata muhimmiyar rawa wajen cimma muradan na su Tinubu
FCT, Abuja - Al'umma dai duk sun shaida cewa Tinubu ya kai ziyara ne ga Wike domin buɗe ayyukan da ya gudanar. Sai dai wata ƙungiya na ganin akwai wani abin a ƙasa da jama'a ba su fahimta ba.
Wata ƙungiyar rajin tabbatar da bin doka da oda mai zaman kanta CRPA, ta ce babban dalilin zuwan Tinubu Rivers shine domin ya baiwa Wike aikin lalata duk wasu hujjoji da Atiku da Peter Obi za su dogara da su a shari'ar ƙorafin zaɓen da su ka shigar da Tinubun a gaban kotu.
Wike ya na so a dama da shi a gwamnatin Tinubu
A cewar ƙungiyar, akwai alamu da ke nuni da cewa matar gwamna Wike wato mai shari'a Eberechi Suzzette Wike, za ta taka wata muhimmiyar rawa wajen cimma ƙudurin na su kamar yadda Legit.ng ta samu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ifeanyi Okechukwu, kakakin ƙungiyar ta CRPA ya ce an zaɓi Wike ya yi aikin ne duba da yanayin yadda ya zaƙu da ya shiga a dama da shi a cikin gwamnatin Tinubu.
Okechukwu ya ƙara da cewar ko gine-ginen kotu da Wike ya ƙaddamar a jihar ta Rivers, ya yi su ne domin tabbatar ma da jam'iyyar APC da kuma Tinubu cewa zai iya yin aikin na rusa duka hujjojin da Atiku da Obi su ke da su.
Matar Wike za ta taka muhimmiyar rawa wajen yaƙar Atiku
Haka nan ƙungiyar ta ce ta samu bayanai da ke nuni da cewa, matar ta Wike mai shari'a Eberechi Suzzete Wike za ta taka muhimmiyar rawa a cikin shirin na su da su ke shiryawa kan yaƙar Atikun.
Okechukwu ya ƙara da cewa su Tinubu su na ganin kamar Wike ne ya fi dacewa da ya yi musu wannan aiki saboda ganin kamar cewa Wike ya zame ma Atiku ƙarfen ƙafa, wanda su ke ganin kuma zai iya lalata duk wasu hujjoji da Atiku zai yi taƙama da su.
Rikicin PDP: Atiku da Wike za su haɗu a Abuja
Akwai yiwuwar Atiku da Wike su halarci wani taro da ƙungiyar gwamnonin PDP ta shirya a Abuja.
Gwamnan jihar Sokoto, kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin wato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ne dai wanda zai jagoranci taron.
Ana sa ran cewa taron zai gudana a ranar Alhamis, 11 ga watan Mayun 2023, a ɗakin taro dake Otel ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja babban birnin tarayya.
Asali: Legit.ng